Hadimin Buhari ya goyi bayan Zulum da dalilai, ya ce Borno ta samu cigaban tsaro
- Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi bayan Gwamna Zulum
- Ya ce an samu manyan cigaba a fannin tsaro a jihar Borno a yayin mulkin Buhari
- Kamar yadda yace, rayuwa ta koma daidai a wasu sassan Borno wanda a da ba haka bane
Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya goyi bayan kalaman gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.
Gwamnan ya bayyana cewa duk da yadda ake ta cece-kuce a kan tsaron kasar nan, Borno ta samu cigaba a fannin tsaro a mulkin Buhari.
Lamarin ya janyo cece-kuce daga jama'a, inda suke sukar abinda Zulum yace.
Kamar yadda Bashir Ahmad yace, "An samu sauyi masu tarin yawa karkashin mulkin shugaba Buhari.
"Sauyin sun hada da ceto 'yan matan Chibok sama da 100, sarakuna sun koma masarautunsu, an kwato wasu kananan hukumomi, an dawo da wutar lantarki, makarantu, filin jirgin sama, filayen wasanni an bude, an cire dokar ta baci.
"Za mu iya mantawa, amma gaskiya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kokari."
KU KARANTA: Tsohon sanatan Adamawa, Nyako, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
Kamar yadda Zulum ya bayyana, ya ce ana samun tashin bama-bamai a wasu sassan Maiduguri amma duka hakan ya tsaya bayan hawan mulkin Buhari. Babu shakka wannan tarihi ne da ya kafa wanda babu ja-in-ja.
Ya kara da cewa, a yanzu an koma rayuwa a Bama, Askira-Uba, Damboa, Gwoza da sauransu. Ana komawa Baga a halin yanzu. Duk hakan ta yuwu ne sakamakon kokarin Buhari.
KU KARANTA: Yadda Boko Haram suke amfani da fasahar Intanet wurin watsa bidiyoyi
A wani labari na daban, da yawa daga cikin daliban makarantun allo, wadanda aka fi sani da Almajirai, wadanda ke yawo a titunan arewacin kasar nan ba 'yan Najeriya bane a cewar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.
"Da yawansu daga kasashen ketare suke kamar jamhuriyar Nijar, Chadi da Kamaru," Ganduje yace yayin bude taron kwanaki uku da UBEC take a jihar Kano.
"Daga binciken da muka yi, da yawa daga cikin almajiran da ke yawo a titunanmu daga kasashen Nijar, Cahdi da Kamaru suke," yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng