Yajin aiki: Mun cika wa ASUU dukkan alkawurran da muka dauka, FG

Yajin aiki: Mun cika wa ASUU dukkan alkawurran da muka dauka, FG

- Gwamnatin tarayya ta musanta maganar da shugaban ASUU yayi a ranar karshen mako

- Ta ce tana kan hanyar cika duk alkawuran da ta daukar wa ASUU, ta ma cika wasu yanzu haka

- Sannan sun yi da ASUU cewa za ta janye yajin aikinta a ranar 9 ga watan Disamba kuma za ta biya su albashi

A jiya ne gwamnatin tarayya ta nuna takaicinta a kan maganganun da shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi yayi a kan yadda yace gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta daukar wa kungiyar.

ASUU ta ce malaman jami'a ba za su koma makarantu babu abinci ba. Amma ministan kwadago da ayyuka, Sanata Chris Ngige ya ce tabbas an cika wasu daga cikin alkawuran da gwamnati ta daukar wa ASUU, Vanguard ta ruwaito.

Ofishin yada labaran ministan yace, "Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin za ta shigar da kwamitin sasanci na yarjejeniyar 2009 sannan kuma ta cika alkawarin da ta daukar wa kwamitin da farfesa Munzali yake shugabanta.

Yajin aiki: Mun cika wa ASUU dukkan alkawurran da muka dauka, FG
Yajin aiki: Mun cika wa ASUU dukkan alkawurran da muka dauka, FG. Hoto daga @Vangauardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda Boko Haram suke amfani da fasahar Intanet wurin watsa bidiyoyi

"Ana ta kokarin ganin an bayar da naira biliyan 70 da gwamnati ta amince za ta biya ASUU. Sannan shugaban kasa ya amince da kwamitin ziyara da duba ayyukan jami'o'i, amma kwamitin ba za ta fara aiki ba, har sai makarantu sun bude.

"Ana kokarin kammala takardu a ofishin Antoni janar, sannan ministan ilimi a shirye yake da ya zabi 'yan kwamiti ziyarar.

"Gwamnati ta amince da biyan albashin ma'aikata da sauran kudade ta wani tsari wanda ba zallar IPPIS bane, sannan kuma ana nan ana gwada ingancin UTAS da NITDA kamar yadda ASUU ta bukata. Don haka duk wani alkawari da gwamnati ta dauka ta cika shi.

KU KARANTA: Da yawan almajiran da ke tituna ba 'yan Najeriya bane, Gwamna Ganduje

Hakazalika ministan ya tabbatar wa da duniya cewa sun yi da ASUU cewa za ta janye yajin aikinta a ranar 9 ga watan Disamban 2020, kuma FG za ta biya albashin malamai zuwa ko kuma kafin ranar da suka koma makarantu.

A wani labari na daban, Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar APC, ya ce idan aka bashi damar shugabantar jam'iyyar ba zai yi ba.

A ranar Litinin, Oshiomhole ya ce yana matukar alfahari da yadda NWC tayi aiki a karkashin mulkinsa, The Cable ta wallafa.

Oshiomhole ya ce bai riki kowa ba a zuciyarsa, har wadanda suka shiga suka fita har aka tumbuke shi daga mukaminsa ba, hasalima ya umarci lauyoyinsa da su janye korafin da ya tura a kan dakatar dashi da aka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng