Ba zan saka kaya kamar 'yar kauye ba saboda ina da aure, Matar aure ga kotu

Ba zan saka kaya kamar 'yar kauye ba saboda ina da aure, Matar aure ga kotu

- Wani Sheriff ya zargi matarsa Rashidat da yin lalata da wani dan sanda, don haka ya bukaci kotu ta raba aurensu

- A cewarsa, tana yin shiga kamar ba matar aure ba, kuma tana lalata da wani dan sanda duk da Rashidat ta musa

- Ta ce ya mayar da ita tamkar jaka, sannan ya sadu da ita ta karfi da yaji, har idonta na hagu ya makantar mata

Rashidat, matar Sheriff Ahmed, mai shekaru 44, ta zargi mijinta da takura mata a kan yadda take shiga. Ahmed ya maka matarsa a kotu, inda yake bukatar su rabu sakamakon rashin kamun kanta da kuma mummunar shiga.

Ya kai korafin a wata kotu da ke Igando ranar Litinin, inda ya zargeta da lalata da wani dan sanda, The Cable ta wallafa.

A cewarsa, ya so ya fatattaki matarsa, amma yadda 'yan uwa da abokan arziki suka sanya baki yasa ya hakura.

Kamar yadda NAN ta ruwaito, "Matata bata da kamun kai, har lalata take yi da wani dan sanda.

"Da na duba wayarta, na ga yadda take kalaman iskanci da soyayya da wannan dan sandan ta kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp.

Ba zan saka kaya kamar 'yar kauye ba saboda ina da aure, Matar aure ga kotu
Ba zan saka kaya kamar 'yar kauye ba saboda ina da aure, Matar aure ga kotu. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

"Har fada muka yi akan hakan, na so in fatattaketa amma saboda 'yan uwa da abokan arziki sun sanya baki, na yafe mata.

"Tana sanya sutturu wadanda basu dace da matar aure ba. Na roke ta a kan ta canja shigarta, da rayuwarta, amma ta ki."

Ahmed ya zargi matarsa da yawo da layu a jakarta, sannan tana fita a duk lokacin da ta ga dama. Ya bukaci kotu ta raba su don yanzu ta fita daga ransa.

Rashidat tace wa kotu ta amince da a kashe aurenta, don ta gaji. Matar mai yara 2 ta musanta yin lalata da dansanda, inda tace kishin mijinta ya yi yawa.

Ta zargi Sheriff da ci mata mutunci da kuma saduwa da ita ta karfi da yaji.

"Ya mayar da ni kamar jakarsa, sannan ya sadu dani ta karfi da yaji bayan ya gama dukana," a cewarta.

KU KARANTA: Matashin likita tare da abokinsa sun kone kurmus a hatsarin mota a Katsina

"Sai da ya zubar min da ciki sau 2, saboda duka. Sakamakon duka, har idona na hagu na rasa, duk da an yi min aiki, amma har yanzu ba na gani."

Ta ce ya sha dukanta kamar zai kasheta ana tafiya da ita asibiti, shiyasa ta gudu saboda zai iya kasheta watarana.

Alkalin ya raba auren Sheriff da Rashidat, sannan ya bai wa Rashidat damar rike yaran. Sheriff zai dinga ba ta N10,000 duk wata kuma ragamar karatu da walwalar yaran tana wuyansa.

KU KARANTA: ASUU ta gindaya wa gwamnatin tarayya sabon sharadin komawa aiki

A wani labari na daban, wani bidyo da yake nuna shugaban ma'aikatan fadar gwamna jihar Abia, Anthony Agbazuere yana zuba wa wani fasto mai suna Odumeje wanda aka fi sani da Indaboski ya janyo cece-kuce.

A bidyon da wani mai suna Enwagboso ya wallafa a shafinsa na Twitter, an ga Agbazuere yana watsa wa Chuwuemka Ohanaremere wanda aka fi sani da Odumeje kudi.

A bidiyon, ba a ga wacce rana lamarin ya faru ba, amma ya bayyana cewa a ofishin Agbazuerre ya faru, Channels Tv ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng