Rashin tsaro: Gwamnonin APC sun shawarci Buhari a kan bayyana a gaban majalisar tarayya

Rashin tsaro: Gwamnonin APC sun shawarci Buhari a kan bayyana a gaban majalisar tarayya

- Gwamnonin jam'iyyar APC basa son shugaba Buhari ya zauna da 'yan majalisar tarayya a kan harkar tsaro

- A cewar gwamnonin, matsawar ya zauna dasu zai janyo raini gare shi, su dinga bukatar zama dashi a kan kananun abubuwa

- Gwamnonin sun yanke shawarar zaunawa da 'yan majalisun jihohinsu, amma babu tabbas idan har da 'yan jam'iyyun adawa

A kan taron APC NEC, gwamnonin jam'iyya mai mulki sun yi wani taro a ranar Litinin da yamma, inda suka tattauna a kan makasudin taron da za a yi na NEC.

A taron, Premium Times ta gano cewa gwamnonin sun hada kai a kan hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zaunawa da 'yan majalisar tarayya a kan batun rashin tsaron da ke kasar nan.

Sun ce hakan zai iya janyo wa shugaban kasa raini, ta yadda 'yan majalisar tarayya za su dinga kiransa taro a kan kananun abubuwa.

Rashin tsaro: Gwamnonin APC sun hana Buhari bayyana a gaban majalisar tarayya
Rashin tsaro: Gwamnonin APC sun hana Buhari bayyana a gaban majalisar tarayya. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Oshiomhole ya bayyana abinda zai yi idan ya samu damar sake shugabancin APC

Sannan sun ce za su tayar da wannan maganar a taron NEC da za su yi. Gwamnan jihar Ondo, Mr. Akeredolu, ya nuna amincewarsa a kan wannan batun.

NEC ta kawo wannan shawarar, sannan ta umarci gwamnoni da su zaunar da 'yan majalisar jihohinsu su tattauna dasu a kai.

Ga dukkan alamu gwamnonin APC za su yi taro da 'yan majalisar tarayya. Amma ba a san me za su tattauna ba a taron.

KU KARANTA: Ba zan saka kaya kamar 'yar kauye ba saboda ina da aure, Matar aure ga kotu

Ba a kuma san ko za su gayyaci sauran yan majalisar da ke karkashin jam'iyyun adawa ba, ko kuma menene makomarsu saboda canja shawarar.

An yi kokarin neman Yekini Nabena, mataimakin kakakin jam'iyyar APC na kasa, don jin ta bakinsa, amma abin ya ci tura don bai amsa kiran da aka yi masa ta waya ba, kuma bai mayar da martani a kan sakon da aka tura masa ta waya ba.

A wani labari na daban, Shugaban ACF, Audu Ogbeh, ya ce harkar tsaron arewa kullum tabarbarewa take yi. Ogbeh ya jagoranci mutane zuwa Maiduguri don jajanta wa gwamnan a kan kashe-kashen Zabarmari.

Fiye da manoma 40 'yan Boko Haram suka kashe a kauyen da ke karkashin karamar hukumar Jere a makonnin da suka gabata, The Cable ta wallafa.

Tsohon ministan ya ce babbar matsalar da ke addabar arewa shine yadda aka mayar da siyasa ta zama hanyar da kowa yake son ya samu kudi da ita. Ya kara da cewa siyasa kuwa bata samar da cigaba a ko ina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel