Hazikan sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram, sun kashe guda 9

Hazikan sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram, sun kashe guda 9

- Rundunar sojojin Najeriya ta kashe 'yan kungiyar Boko Haram guda tara tare da jikkata wasu da dama

- Hazikan sojin sun cimma wannan gagarumin nasarar ne cikin kwanaki biyu a jihar Borno

- An kuma samo wasu kayayyaki da suka hada da hatsi da buhuhunan bushasshen kifi

Dakarun sojojin Najeriya na Operation Lafiya Dole sun yi gagarumin nasara a kan mayakan Boko Haram a jihar Borno.

A bisa ga wata sanarwa da hedkwatar tsaron kasar ta fitar, ta ce dakarun nata sun halaka yan ta’addan na Boko Haram su tara tare da jikkata wasu da dama cikin kwanaki biyu.

A cewar sanarwar, a ranar Talata, 8 ga watan Disamba, bayan samun rahotanni na sirri kan zirga-zirgan mayakan daga garuruwan da ke iyakar Sambisa, dakaru na musamman da ke Pulka sun yi nasarar kai masu harin bazata a mararrabar Pulka-Firgi-Banki.

Hazikan sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram, sun kashe guda 9
Hazikan sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram, sun kashe guda 9 Hoto: @DefenceInfoNG
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo

A yayin fafatawar sun kashe mayaka hudu. An kuma kwato wasu kekuna biyu, amalanke biyu, buhuhunan busasshen kifi, hatsi da sauran kayayyakin abinci masu tarin yawa.

A wannan ranar kuma dakarun sun kashe yan kungiyar guda uku a kan titin Firgi-Pulka, sannan suka raunata wasu da dama.

Har ila yau, a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, sojojin sun halaka wani mayakin Boko Haram daya a garin Mogoniri bayan samun rahotannin sirri kan ayyukan yan ta’addan.

Haka nan an kashe wani mayakin a Gonori da ke kusa da Dajin Sambisa duk a Litinin din, an kuma samo bindigar AK 47 daya, mujalla da babu komai ciki daya da wayar salula kirar tecno.

KU KARANTA KUMA: Fatai Aborode: An harbe wani jigon PDP har lahira a jihar Oyo

A wani labarin, Dan majalisar dokokin jihar Taraba, Bashir Bape, da aka yi garkuwa da shi ya samu yanci a daren Juma'a, majiya daga hukumar yan sanda da iyalansa sun tabbatar.

A cewar rahoton Premium Times, har yanzu ba a san ainihin adadin kudin da aka biya kudin fansa ba amma majiya daga gidan dan majalisan ya bayyana cewa: "an biya kudin fansa kafin aka sakeshi."

"An sake shi a daren jiya misalin karfe 10 na dare, kuma yanzu yana asibiti. Muna godiya ga dukkan wadanda suka taya mu addu'a," ya kara. sace.html

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel