Mutumin da ya fi kowa arziki a kasar Brazil ya rasu

Mutumin da ya fi kowa arziki a kasar Brazil ya rasu

- Mashahurin attajirin Brazil dan asalin kasar Lebanon Joseph Safra, ya rasu ranar Alhamis ya na da shekara 82, a cewar bankin sa

- An haife shi a 1938 ga wasu iyalai Yahudawa a Beirut, ya yi hijira shi da Iyalan sa zuwa Brazil, inda mahaifin sa ya samar da inda ake kira Banco Safra

- Mutumin shine na 63 a jerin masu kudin duniya kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa

Mashahurin attajirin Brazil dan asalin kasar Lebanon Joseph Safra, ya rasu ranar Alhamis ya na da shekara 82, a cewar bankinsa

Safra, wanda kiyasin dukiyar ya kai kimanin $23.2 biliyan, wanda ya zo na 63 cikin jerin masu kudin duniya da mujallar Forbes ta fitar.

Mutumin da ya fi kowa arziki a kasar Brazil ya rasu
Mutumin da ya fi kowa arziki a kasar Brazil ya rasu. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade

An haife shi a 1938 ga wasu iyalai Yahudawa a Beirut, yayi hijira shi da Iyalan sa zuwa Brazil, inda mahaifin sa ya samar da inda ake kira Banco Safra.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ƙara matasan da za a ɗiba a N-Power zuwa miliyan ɗaya

A 1962, shi da dan uwansa sun ci gaba da kula da bankin mahaifinsu, wanda ya rasu bayan shekara guda.

Sun maida shi babban cibiyar hada hada, in da ya fara aiki a kasashe fiye da 25.

Ya na son zayyana kuma mutum ne mai taimako, Safra ya sadaukar da wani bangare na dukiyar sa ga masu binciken lafiya, kuma ya sayi wasu aikin zayyana da adanawa a Sao Paulo's Pinacoteca, wani babban gidan adana kayan tarihi a Brazil.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel