Zulum ya roƙi Buhari ya tallafawa ƴan gudun hijira 200,000 su koma gidajensu

Zulum ya roƙi Buhari ya tallafawa ƴan gudun hijira 200,000 su koma gidajensu

- Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya roƙi gwamnatin tarayya ta tallafa wurin mayar da yan gudun hijira gidajensu

- Zulum ya ce akwai ƴan asalin jihar Borno kimanin 200,000 a ƙasashen Chadi, Kamaru da Nijar da ke son dawowa gida

- Gwamna Zulum ya ce a shirye gwamnatin jihar Borno take don hadin gwiwa da gwamnatin tarayya don dawo dasu gida

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya roƙi gwamnatin tarayya da Shugaba Buhari ke jagora ta taimakawa ƴan gudun hijiran Najeriya kimanin 200,000 da ke Nijar, Kamaru da Chadi su dawo gida.

Mista Zulum ya yi wannan rokon ne a ranar Juma'a a Abuja cikin jawabin da ya yi wurin taron masu ruwa da tsaki kan taimakawa ƴan gudun hijira, Vanguard ta ruwaito.

Zulum ya roƙi Buhari ya tallafawa ƴan gudun hijira 200,000 su koma gidajensu
Zulum ya roƙi Buhari ya tallafawa ƴan gudun hijira 200,000 su koma gidajensu. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

Ya bayyana taron a matsayin abin yabawa da jinjinawa.

"Ƴan gudun hijira kimanin 200,000 ƴan asalin jihar Borno da ke zaune a Kamaru, Chadi da Nijar suna son dawowa gida. Sun daɗe suna neman a dawo da su gidajensu.

"Sun ma sako ni a gaba. Ina roƙon gwamnatin tarayya ta taimaka. Gwamnatin Borno a shirye ta ke ta haɗa gwiwa da gwamnatin tarayya ta hannun Ma'aikatan Jin Ƙai.

"Muna iya yin hakan da nufin nemo inda za a dawo da su cikin mutunci," in ji Mista Zulum.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe Kanawa 16 a titin Kaduna zuwa Abuja

Gwamnan na kyautata tsammanin cewa bayan taron masu ruwa da tsakin za a samar da hanyar da ta dace na inganta rayuwarsu da dawo da su gida.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel