Pantami na son maida da Abuja 'smart city'

Pantami na son maida da Abuja 'smart city'

- Pantami yana shirin maida Abuja birnin da ke amfani da kimiyya da fasaha don saukaka al'amura da tsaro

-Ya bayyana cewa ya tuntubi ministan Abuja kan batun kuma tuni shiri yayi nisa

-Ya bayyana hakan ne a wani taron baje kimiyya da fasaha da aka kammala a Dubai, UAE

Ministan sadarwa ta tattalin arzikin zamani, Dr Isa Pantami ya yi kira da a maida babban birnin tarayya Abuja birni mai amfani da fasahar zamani don gogayya da manyan birane a ci gaban fasahar duniya.

Ma'anar 'smart city' shine birni da ke amfana da fasahar zamani wurin gudanar da ayyuka da kuma magance matsalolin da ke adabar birnin, kamar yadda ma'anar yake a shafin google.

Pantami na son Abuja ta koma 'birnin kimiyya'
Pantami na son Abuja ta koma 'birnin kimiyya'. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC

Birnin yana yin abubuwa kamar saukaka tafiye tafiye, taimakawa wajen ci gaban mutane, taimakawa wajen sana'o'i, da kuma taimakawa matsalolin mutane.

Da ya ke jawabi a wajen rufe taron 'Gulf Information Technology Exhibition, GITEX', na wannan shekarar a Dubai, Babbar Daular Larabawa, UEA, Pantami ya ce baya ga saukaka rayuwa, zai kuma taimaka wajen inganta tsaro.

Kawo yanzu, Pantami ya tattauna da ministan Abuja Mohammad Bello kan batun, ya kuma tabbatar da ministan ya gamsu da maida Abuja irin wannan birni.

KU KARANTA: Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

Ya ce: "na ziyarci ministan Abuja da wannan batu na maida Abuja 'birnin fasaha' ko kirkirar wani sabo da zai zama mai amfani da kimiyyar zamani.

"Muna da gwamnoni masana fasaha da nake so su shiga tsarin, zan basu shawara da kuma karfafa musu gwiwa kan yadda za ayi.

"Tuni muna da masu zara gine ginen kimiyya kuma har sun fara aikin ganin yadda za su gudanar da aikin, wanda za a gwada daya cikin watan Disamba.

"Wannan na nufin zamu iya haure rukunin gidaje zuwa babban gari idan abin ya yiwu."

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel