Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya
- A yau 11 ga watan Disamba ne Ahmed Indimi, mijin Zahra ɗiyar shugaba Buhari ke bikin zagayowar ranar haihuwarsa
- Zahra ta wallafa hoto da rubutun soyayya da fatan alheri don taya mijinta murnar ranar
- A cikin rubutun da ta wallafa, Zahra ta ce ranaku biyu da suka fi faranta mata rai sune ranakun zagayowar ranar aurensu da na haihuwar mijinta
Ɗiyar Shugaba Buhari, Zahra Buhari Indimi, tana cikin farin ciki a yau 11 ga watan Disamba a kasancewar ranar zagayowar haihuwar mijinta, Ahmed Indimi.
Zahra wacce ke da ɗa guda kuma ke ɗauke da cikin na biyu ta wallafa rubutu a shafinta na Instagram inda ta yi wa mijinta fatan alheri.
DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun ce sun kashe kasurgumin dan bindiga a Niger
Ta kuma wallafa wani hoto da ke nuna ta tare da mijinta a yayinda suke tattaunawa cikin nishaɗi.
Wani sashi na abinda ta rubuta ya ce;
"Ban san abinda ka ke ƙoƙarin yin bayani ba a nan amma ina son ka sani cewa ina amfana da ilimi da hikima daga gare ka.
"Ban taɓa ganin wadda ke ƙara shekaru ba amma kuma yake ƙara kyau kamar ka. Na san son kai nayi amma babu lokacin da yafi wannan dacewa da yin hakan."
KU KARANTA: Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC
Zahra ta cigaba da cewa watan Disamba wata ce na farin ciki a gidansu saboda bikin zagayowar haihuwar mutane da dama ga shi kuma ya fado a ranar Juma'a.
Ta cigaba da cewa bukukuwan da ta fi so sune bikin zagayowar ranar haihuwar mijinta da na ranar aurensu.
Daga ƙarshe ta yi addu'ar Allah ya tsare shi ya cigaba da sanya albarka a rayuwarsa.
A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.
The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.
Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng