Majalisa ta ce an saye biron N14.5m, takardun N46m a Ma’aikar man fetur

Majalisa ta ce an saye biron N14.5m, takardun N46m a Ma’aikar man fetur

- Sanatoci suna binciken zargin badakalar da aka yi a Ma’aikatar man fetur

- An bada kwangilolin fiye da N115m domin shigo da biro da kuma takardu

- Ma’aikatar tace ba ta saba wata doka a lokacin da ta bada kwangilolin ba

Majalisar dattawa ta bayyana badakalar da ake zargin da an tafka a ma’aikatar mai a gwamnatin tarayya, jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto.

Sanatocin ta bakin Matthew Urhoghide sun bayyana cewa an bada kwangilar Naira miliyan 14.5 domin a kawo biro samfurin Schneider a ma’aikatar.

‘Yan majalisar tarayyan sun kuma bayyana cewa an bada kwangilar Naira miliyan 46 domin ayi aikin takardu masu tambarin ma’aikatar ta man fetur.

Ba a nan kadai binciken na Sanata Urhoghide ya nuna ba, ma’aikatar gwamnatin ta kashe Naira miliyan 56 wajen sayen garin na’ura na buga takardu.

KU KARANTA: Matthew Urhoghide ya shiga uku bayan ya nemi a tsige Buhari

Sanata Matthew Urhoghide mai wakiltar Edo ta kudu a majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar PDP, shi ne shugaban kwamiti na binciken batar da kudi.

Wannan kwamiti ya dogara ne da korafin da ofishin babban mai binciken kudi na kasa ya yi a 2015.

A lokacin, babban mai binciken kudi na tarayya yana zargi an datsa wannan kwangila na biro zuwa bangare uku domin a samu damar aika-aikan da za ayi.

Wajen bada kwangilar N46m na buga takardu masu tambari, an raba wa kamfanoni 11 wannan aiki, haka kamfanoni 7 su ka samu kwangilar sayo 'tonner'.

KU KARANTA: Sanata Mathew Urhoghide ya canji Fatima Raji-Rasake a kwamiti

Majalisa ta ce an saye biron N14.5m, takardun N46m a Ma’aikar man fetur
Majalisa ta na zama Hoto: Twitter/@NgrSenate
Source: Facebook

Ma’aikatar tarayyar ta maida martani, ta sanar da majalisa cewa babu tambayar da za ta amsa domin an bi ka’idojin aiki wajen bada wadannan kwangiloli.

A baya mun kawo maku jerin Sanatocin da su ka fi yawan kudiri a majalisar dattawan Najeriya.

Sanatocin da ke kan gaba su ne Mohammed Sani Musa, Ifeanyi Patrick Ubah, Ali Ndume, Istifanus Gyang, Gershom Henry Bassey, Olamilekan Adeola da Buhari Abdulfatai.

Ragowar su ne: Opeyemi Bamidele, Ike Ekweremadu, Ibrahim Barau Jibrin, Aliyu Sabi Abdullahi , Betty Apiafi, Uba Sani, Ibikunle Amosun, Ibrahim Yahaya Oloriegbe.

Sai kuma Kashim Shettima, Bassey Albert Akpan da irinsu Kwamred Abba Patrick Moro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel