Nigerian news All categories All tags
Bayan matasa sun suburbudeshi, Sanatan da yayi kira ga tsige Buhari na fuskantar kiranye daga mazabarsa

Bayan matasa sun suburbudeshi, Sanatan da yayi kira ga tsige Buhari na fuskantar kiranye daga mazabarsa

Kungiyar matasan yankin Edo ta kudu sun lashi takobin kaddamar da shirin kiranyen Sanata Matthew Urhoghide bisa ga kiran da yayi a zauren majalisa cewa a tsigr shugaba Muhammadu Buhari.

Kungiyar matasan sunce abun da kawai zai iya hanasu hakan shine idan ya janye maganarsa.

Sanata Matthew Urhoghide mai wakiltan mazabar Edo ta kudu ya yi kira gay an Majalisan dattawa a ranan Alhamis cewa a tsige shugaba Muhammadu Buhari.

Amma a rantsar Asabar, ya yi bayanin cewa shi bai fadi haka ba; innama cewa kawai yayi abinda shugaba Buhari yayi na kashe kudi ba tare da izinin majalisa ba laifi ne da ya cancanci kiranye.

Bayan matasa sun suburbudeshi, Sanatan da yayi kira ga tsige Buhari na fuskantar kiranye daga mazabarsa

Bayan matasa sun suburbudeshi, Sanatan da yayi kira ga tsige Buhari na fuskantar kiranye daga mazabarsa

Zaku tuna cewa a ranan Juma’a, matasan mazabarsa suka suburbudeshi a filin jirgin saman Benin daga dawowarshi daga Abuja.

KU KARANTA: Shekarau ya shirya fitowa takarar shugaban kasa a PDP

Sanata Matthew Urhoghide ya zargi mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibum da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Mr Taiwo Akerele, ne suka shirya matasan APC su ci masa mutunci.

Matasan sun baiwa sanatan awanni 48 ya janye maganarsa ko kuma ya fuskanci kiranye.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel