Jami’in Banki ya fadawa Alkali kudin da aka zuba a asusu a karar Fayose v EFCC

Jami’in Banki ya fadawa Alkali kudin da aka zuba a asusu a karar Fayose v EFCC

- Wani Jami’in banki ya bayyana a matsayin shaidan EFCC a shari’ar Ayo Fayose

- Ana zargin tsohon gwamnan da wawurar wasu Naira biliyan 2.2 daga baitul mali

- Ba a iya samun sunan Ayodele Fayose ya fito a hujjojin da shaidan ya gabatar ba

An cigaba da sauraron shari’ar da ake yi tsakanin hukumar EFCC da tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose da kamfanin Spotless Investment Limited.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, Kotu ta saurari shaida na tara da EFCC ta gabatar, wani ma’aikacin babban banki.

Babban Lauyan da ya tsaya wa EFCC, Rotimi Jacobs (SAN), ya gabatar da wannan shaida a kotu, Taiwo Ogundein ya yi wa Alkali bayanin duk abin da ya sani.

KU KARANTA: Alkali ya yi fatali da karar Walter Onnoghen da Gwamnati

Taiwo Ogundein ya bada labarin yadda aka rika shiga da kuma fitar da makudan kudi daga asusun kamfanin Still Earth Limited a lokacin Ayo Fayose ya na mulki.

Daga cikin zargin da EFCC ta ke yi shi ne Ayo Fayose ya saye gidan Naira miliyan 200 a Abuja ta hannun wani babban banki da sunan wata mata, Misis Moji Oladeji.

Mista Ogundein ya shaidawa Alkali cewa shi ne ke kula da asusun kamfanin Still Earth Limited a banki, kuma an taba zuba wasu miliyoyi a cikin asusun a 2015.

Ogundein ya tabbatar da cewa an jefa N40m, N39.5m, N70.7m, N132m, N200m, N47m a wannan asusu tsakanin Junairun 2015 zuwa watan Fubrairun shekarar.

KU KARANTA: Mun ba Ndume mako 3 ya fito da Maina - Kotu

Jami’in Banki ya fadawa Alkali kudin da aka zuba a asusu a karar Fayose v EFCC
Ayodele Peter Fayose Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

Ko da wannan ya faru a lokacin da Fayose ya ke gwamna, babu inda sunansa ya fito a cinikin da aka rika yi kamar yadda Lauyoyinsa su ka tabbatar wa Alkali.

Bayan sauraron Ola Olanipekun da Olalekan Ojo, Alkali C.J. Aneke ya daga karar zuwa yau.

A kwanakin baya, wani ma’aikacin banki mai suna Olugbenga Falai, ya fadawa kotu yadda aka jefa Naira miliyan 200 zuwa asusun kamfanin Still Earth Limited.

Ana cikin wannan shari'a ne ku ka ji cewa an canza Alkalin da ke binciken Ayo Fayose a Kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel