Cutar COVID-19 ta jawo Ayo Fayose da Gwamna Kayode Fayemi a kan tebur a Ekiti

Cutar COVID-19 ta jawo Ayo Fayose da Gwamna Kayode Fayemi a kan tebur a Ekiti

A dalilin cutar COVID-19, tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose da kuma magajinsa watau mai girma gwamna Kayode Fayemi sun ajiye banbancin siyasarsu a gefe guda.

Gwamna Kayode Fayemi ya kafa wani kwamiti da zai yi yaki da cutar Coronavirus watau COVID-19 a Ekiti. Wannan kwamiti ya na kunshe da mutane 47 da aka zakulo daga jihar.

Daga cikin wadanda aka sa a cikin wannan kwamiti akwai duk tsofaffin gwamnonin Ekiti wanda su ka hada da gawurtaccen ‘dan adawan gwamna mai-ci da kuma APC, Fayose.

Mista Ayodele Peter Fayose shi ne wanda ya sauka daga kan mulki a jihar Ekiti a tsakiyar shekarar 2018, kuma ya mika kujerar ga gwamna mai-ci Kayode Fayemi na jam’iyyar APC.

Abin mamaki shi ne Ayo Fayose ne ya doke Kayode Fayemi a zaben gwamnan da aka yi a 2014. Fayose wanda ya yi mulki a shekarun baya ya kifar da APC a lokacin ya koma kujera.

KU KARANTA: Bincike ya nuna Maza sun fi Mata kamuwa da Coronavirus a Najeriya

Cutar COVID-19 ta jawo Ayo Fayose da Gwamna Kayode Fayemi a kan tebur a Ekiti

Gwamna Kayode Fayemi ya sa Fayose cikin kwamitin yaki da COVID-19
Source: Depositphotos

Ragowar tsofaffin gwamnonin da aka jefa cikin wannan kwamiti su ne Otunba Niyi Adebayo da kuma Cif Segun Oni. Kwanaki ne Segun Oni ya tsere daga APC ya koma jam’iyyar PDP.

Shi kuma gwamnan jihar Ekiti na farko a tarihi watau Niyi Adebayo, minista ne yanzu a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kafin nan ya na cikin shugabannin APC.

Biyu daga cikin wadannan tsofaffin gwamnoni su na tafiyar jam’iyyar adawa ne a kasar. Amma ganin cewa wannan annoba ta shafi kowa, su ka ajiye sabanin akidar su domin a ceci jihar.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Prince Julius Adelusi-Adeluyi wanda shi aka ba kujerar shugaban kwamitin. Aare Afe Babalola ya na cikin sauran ‘yan wannan kwamitin mutum 47.

Kafin yanzu Dr. Fayemi da Fayose sam ba su ga maciji da juna. A lokacin da Fayose ya ke gwamna a karon karshe, ya yi yunkurin hana Fayemi sake tsayawa takara amma bai yi nasara ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel