Yaki da ta'addanci: Shugabannin kudu sun soki rage makamin da aka yi wa Janar Adeniyi

Yaki da ta'addanci: Shugabannin kudu sun soki rage makamin da aka yi wa Janar Adeniyi

- Kungiyar shugabannin yankin Kudu ta yi korafi a kan hukuncin da aka yiwa Janar Olusegun Adeniyi da suka ce ya yi kama da bangaranci

- Adeniyi ya wallafa wata bidiyo ne inda ya ce makaman da 'yan ta'adda ke da shi ya fi na sojoji bayan wani hari da 'yan ta'addan suka kaiwa tawagarsa

- Kungiyar ta ce idan ba bangaranci ake nuna wa wane dalili ya hana a hukunta wasu sojojin arewa da ake zargin sun bawa 'yan ta'adda bayanai shekaru 2 da suka shude

Kungiyar shugabannin Kudu da Jihohin Tsakiya, SMBLF, a ranar Alhamis, sun soki hukuncin rage mukami da rundunar soji ta yi wa kwamandan 'Operation Lafiya Dole', Janar Olusegun Adeniyi, da kuma tura mataimakinsa gidan maza na kwanaki 28 da horo mai tsanani.

An samu Adeniyi ne da saba wasu daga cikin dokokin aikin soja duk da cewa ya taba jagorancin yakin da sojojin ke yi da 'yan ta'addan Boko Haram, Vanguard ta ruwaito.

Yaki da ta'addanci: Shugabannin kudu sun soki rage makamin da aka yi wa Janar Adeniyi
Yaki da ta'addanci: Shugabannin kudu sun soki rage makamin da aka yi wa Janar Adeniyi. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

A cikin sanarwar da suka fitar, Yinka Odumakin, Guy Ikokwu, Sanata Bassey Henshaw da Dakta Isuwa Dogo sun nuna mamakinsu kan rashin hukunta sojojin arewa musulmi da ake zarginsu da bawa 'yan ta'adda bayanai da suka yi sanadin kisar wasu sojoji shekaru biyu da suka shude.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe Kanawa 16 a titin Kaduna zuwa Abuja

Kungiyar ta ce: "Janar Adeniyi ya fara fuskantar matsaloli ne bayan ya fara korafi kan cewa an tura shi filin daga don yaki da Boko Haram ba tare da bashi kayan yaki ba.

A baya bayan nan aka fara saka alamar tambaya game da rasa sojoji da rundunar ke yi duk da zunzurutun kudi Naira biliyan daya da aka bawa rundunar soji don sayen makamai.

"Sashi na 15 (g) ta haramta wa sojoji fitar da bidiyo, sautin murya ko hotuna da aka dauka yayin atisaye ko hari."

Amma kotun sojoji ta samu Manjo Janar Adeniyi da laifan shirya da wallafa wani bidiyo kan yaki da ta'addanci a Arewa maso Gabas a wani yanayin da ake yiwa kallon ya kunyata rundunar sojin Najeriya.

KU KARANTA: Tambuwal zai kirkiri Hisbah a jihar Sokoto

Hakan yasa aka rage masa mukami da akalla shekaru uku. Mai tsaronsa, Tokunbo Obanla shima an same shi da laifi an kuma daure shi na kwanaki 28 da horaswa mai tsanani.

Kungiyar ta ce duk da cewa rundunar tana zartar da hukunci da dokokinta suka tanada ne, tayi tambayar dalilin da yasa ba a hukunta sojojin da ake zargin sun bawa 'yan ta'adda bayanan da ya yi sanadin mutuwar sojoji a shekaru biyu da suka shude ba.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel