Matashi ya bayyana yadda abokinsa yayi wuff da budurwarsa bayan ya yi mata alfarma
- Wani saurayi ya wallafa yadda budurwarsa taci amanarsa, ta ja hankalin abokinsa har suka yi aure
- A cewarsa, sai da ya bai wa budurwartasa kudin motar da ta tafi Warri, inda ta hadu da abokinsa ta ha'incesa
- Ya ce daga ya dan hadata da abokinsa don ya kula da ita, yanzu haka sun yi aure har da yara 2
Wani saurayi dan Najeriya ya bayyana yadda budurwarsa ta auri abokinsa bayan ya hadata da shi don ya bata wuri ta kwana a Warri, lokacin da taje wani neman aiki a garin.
A wata wallafa da wani Ikhuoria yayi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ya ce budurwarsa ta je Warri, jihar Delta don neman aiki, sai ta kira shi tana bukatar ya samar mata wurin da za ta zauna.
A cewarsa, sai da ya bai wa budurwar ta sa kudin motan tafiyar, tukunna ta kama hanya. Maimakon ta mayar da hankalinta wurin neman aikin, sai tayi iyakar kokarinta wurin jan hankalin abokinsa.
KU KARANTA: Gayyata zuwa majalisa: Buhari bashi da abiinda zai sanar wa 'yan Najeriya, PDP
Ya ce ya yarda da ita dari bisa dari, amma kawai sai yaji soyayya ta barke tsakaninta da abokinsa. Yanzu haka, ta auri abokinsa, suna zaune lafiya har da yaransu guda biyu.
KU KARANTA: 2023: PDP ta magantu a kan bai wa Jonathan tikitin takarar shugaban kasa
A wani labari na daban, wani magidanci dan kasar Italiya mai suna Forrest Grump an tsince shi yana tsaka da tafiya a yankin Adriatic coast da ke kasar Italiya, jaridar Daily Trust ta wallafa.
Ya bar gidansa da ke Como a makon da ya gabata kafin 'yan sandan da ke Fano su tsare shi. An zarge shi da karya dokar kullen korona tare da sanya masa haraji.
An gano cewa fada yayi da matarsa shine yasa ya fara tattakin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng