Gwamnatin Tarayya ta gaza shawo kan ASUU ta bude Jami’o’i, a koma bakin-aiki

Gwamnatin Tarayya ta gaza shawo kan ASUU ta bude Jami’o’i, a koma bakin-aiki

- Ana cigaba da musayar kalmoni tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya

- ASUU na zargin Gwamnatin Najeriya da kin cika alkawuran da ta dauka

- Ministan kwadago, Chris Ngige yace sai an janye yajin-aiki za a biya kudi

Ministan kwadago da samar da aikin yin a kasa, Chris Ngige ya zargi shugabannin kungiyar ASUU da yin karamar magana bayan zaman da su ka yi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Dr. Chris Ngige yana zargin ASUU da saba alkawari bayan kusan an kai ga yarjejeniyar sake bude jami’o’in gwamnatin kasar.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Chris Ngige ya zabi a sake wani zama tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar malaman jami’o’in a yau.

A ranar Laraban ne ake sa ran cewa Ministan da wakilan gwamnati zasu hadu da bangaren malaman jami’a a Abuja domin cigaba da tattauna lamarin.

KU KARANTA: An hana Malamai albashi tun farkon shekara - ASUU

Idan an hadu, za a duba mas’alolin da aka gaza warware su domin ganin yajin-aikin ya zo karshe.

Ngige ya yi martani game da kalaman da shugaban ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ya yi, inda yake cewa gwamnati ba ta cika alkawuranta ba.

Ministan kwadagon yace sun cika alkawuran da suka dauka, akasin abin da malaman su ke kai.

Chris Ngige ya fitar da jawabi ne ta ofishin yada labaransa, ya ce maganar gaskiya ASUU ce tayi alkawarin za ta janye yajin-aiki a yau, amma ta ki yin haka.

KU KARANTA: Yau ASUU tace za ta janye yajin-aiki - Minista

Gwamnatin Tarayya ta gaza shawo kan ASUU ta bude Jami’o’i, a koma bakin-aiki
ASUU da wakilan Gwamnati a taro Hoto: dailytrust.com
Source: Facebook

A cewar Ministan, da zarar ASUU ta janye yajin-aiki, zai nemi sa-hannun shugaban kasa a biya su ragowar albashinsu kafin ranar 9 ga watan Disamba ta wuce.

Dama can kun taba jin cewa akwai yiwuwar kungiyar ASUU ta dade ta na yajin-aiki. Yanzu wata kusan tara kenan ba a bude jami'o'in gwamnatin tarayya ba.

A ranar Juma’a, 9 ga watan Oktoba, 2020, shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce malamai sun shirya kare martabar jami’o’i, duk inda za a je.

Malaman jami’a sun ce ba gwamnatin kasar ba ta isa ta hana su albashinsu a kan rajistar IPPIS ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel