Yanzu Yanzu: Maina ya yanke jiki ya fadi a yayin shari’arsa a kotu
- Tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, ya yanke jiki ya fadi a kotu
- Maina ya fadin ne yayinda ake ci gaba da shari'arsa a babban kotun tarayya da ke Abuja kan wasu tuhume-tuhume a yau Alhamis, 10 ga watan Disamba
- Zuwa yanzu da ake kawo wannan rahoton, tsohon shugaban hukumar fansho din bai farfado ba
Abdulrasheed Maina, tsohon Shugaban hukumar fansho a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba, ya yanke jiki ya fadi a kotu a yayin shari’arsa, jaridar Tribune ta ruwaito.
Gwamnatin tarayya na shari’a da Maina a kan wasu tuhume-tuhume 12 da ta gabatar gaban wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja.
Tsohon Shugaban fansho din ya yanke jiki ya fadi ne da karfe 10:05 na safe lokacin da lauyansa, Anayo Adibe ke mika shari’arsa a gaban Justis Okon Abang.
KU KARANTA KUMA: PDP ta lashe zaben da aka kammala a jihar Zamfara
Kafin ya yanke jiki ya fadi, lauyansa ya roki kotu a kan ta dage zaman domin bashi damar samun bayanai na zaman da kotu tayi domin ya samu damar shirya takardar babu kara da yake burin gabatarwa a madadin wanda yake karewa.
Sai da kotu ta dage zama ba tare da shiri ba domin ba jami’an hukumar gyara hali damar ba tsohon Shugaban fansho din kulawa.
A daidai lokacin kawo wannan rahoton da misalin karfe 10:30 na safe, Maina bai farfado ba.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage kudin 'Data' da kashi hamsin (50%), Pantami ya sanar
A baya mun ji cewa bayanai sun bayyana a game da yadda aka kama Abdulrasheed Abdullahi Maina, a kasar makwabta, mutumin da ake ta nema a Najeriya.
Vanguard ta ce Abdulrasheed Abdullahi Maina, tsohon shugaban kwamitin da aka kafa domin gyarar harkar fansho ya sulale ne zuwa kasar Nijar.
Jami’an ‘yan sanda a karkashin jagorancin CP Garba Baba Umar ne su ka kutsa har babban birnin Niamey a kasar Nijar, su ka cafke wannan mutumi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng