PDP ta lashe zaben da aka kammala a jihar Zamfara

PDP ta lashe zaben da aka kammala a jihar Zamfara

- Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben da aka karasa na dan majalisa mai wakiltan mazabar Bakura a jihar Zamfara ya lashe zabe

- Hukumar INEC ce ta kaddamar da Ibrahim Tudu a matsayin wanda yayi nasara bayan ya samu kuri’u 23,874

- Babban abokin hamayyarsa na APC, Dan Kande Bello ya samu kuri’u 16,546

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Ibrahim Tudu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben da aka sake na mazabar Bakura a jihar Zamfara.

Baturen zaben, Yahaya Tanko na jami’ar Usmanu Danfodio, Sokoto, ya ce Mista Tudu ya lashe zaben da kuri’u 23,874.

“Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mista Dan Kande Bello, ya samu kuri’u 16,546, yayinda Mista Ibrahim Tudu na PDP ya samu kuri’u 23,874 sannan an kaddamar da shi a matsayin wanda aka zaba,” in ji shi.

PDP ta lashe zaben da aka kammala a jihar Zamfara
PDP ta lashe zaben da aka kammala a jihar Zamfara Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Kakakin majalisar Bauchi ya ce baya shirin barin APC

Shugaban PDP a jihar, Tukur Dan-Fulani, ya zanta da manema labarai jim kadan bayan sanar da sakamakon.

Ya bukaci wanda yayi nasara da ya tabbatar da nasararsa ta hanyar zama jakadan jam’iyyar na gari, jaridar Premium Times ta ruwaito.

A ranar Talata ne APC ta sanar da cewar za ta kauracewa zaben.

Mista Ibrahim Birnin-Magaji, sakataren labaran jam’iyyar a jihar, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta janye ne saboda bata da karfin gwiwa a kan INEC da hukumomin tsaro a jihar.

A baya mun ji cewa, Jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta bayyana matukar mamaki da kaduwarta da samun labarin cewa jam'iyyar APC ta janye daga zaben maye gurbi da za'a kammala a mazabar Bakura, kamar yadda Channels ta rawaito.

KU KARANTA KUMA: Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)

A ranar Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da cewa zaben kujerar dan majalisar jiha na mazabar Bakura bai kammalu ba bayan soke sakamakon wasu mazabu biyar.

Sai dai, tun kafin INEC ta sanar da sabuwar ranar sake gudanar da zabe, jam'iyyar APC ta ce ba zata shiga zaben da za'a kammala ba, ta fice daga takarar neman kujerar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel