Jerin labaran da suka ratsa gari daga watan Junairu zuwa Disamban bana
Shekarar 2020 ta zo wa ‘yan Najeriya da ban mamaki iri-iri. Mun tattaro maku wasu daga cikin manyan labaran da su ka ratsa ko ina a shekarar bana.
Legit.ng Hausa ta tsakuro wasu daga cikin wannan rubutu daga jaridar nan ta The Nation.
1. Shigo da COVID-19
A ranar 25 ga watan Fubrairu ne aka sami wani mutumin kasar Italiya da ya shigo Najeriya dauke da kwayar cutar COVID-19, wannan labari ya tada hankalin ‘yan kasar.
2. Mutuwar Abba Kyari
Jim kadan bayan nan sai aka ji cewa Malam Abba Kyari ya kamu da Coronavirus. A ranar 17 ga watan Afrilu, 2020 ne hadimin shugaban kasar ya rasu a sakamakon jinya.
COVID-19 ta yi sanadiyyar mutuwar Buruji Kashamu da Abiola Ajimobi da wasu manya a bana.
3. Fyade
A shekarar nan an yi ta samun munanan labaran fyade, a haka ne aka tsinci gawar Uwaila Omozuwa a wani coci a garin Edo bayan zargin an yi lalata da ita kafin nan.
An kuma samu wata ‘yar makaranta a Ogun, Grace Oshiagwu da aka yi lalata da ita, har ta mutu.
KU KARANTA: Tsohon Ministan Najeriya, Ismaila Funtua ya mutu
4. Mace-mace a Kano
Daga watan Afrilu ne aka rika samun labaran mace-mace rututu a jihar Kano. Ana zargin mutane fiye da 1000 sun mutu ba tare da an tabbatar da abin da ya kashe su ba.
5. Zanga-zangar #EndSARS
A wannan shekara ne aka yi gagarumar zanga-zangar #EndSARS wanda ya tada jihohin Najeriya. Wannan zanga-zanga da aka yi wa ‘yan sanda ya rikide ya zama tada tarzoma.
Wasu gungun matasa daga Arewacin Najeriya sun fito da na su salon mai taken #SecureNorth.
6. Boko Haram
A wannan shekara an fuskanci hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram, daga ciki akwai kisan matafiya da aka yi a garin Auno, da kisan wasu manoma a Zabarmari, Borno.
7. Garkuwa da mutane
A bana garkuwa da mutane ya yi kamari musamman a Arewacin Najeriya, daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da wasu manyan ‘yan siyasa, wasu sun mutu a dalilin haka.
8. Yajin-aikin ASUU da NLC
A farkon shekarar nan ne kungiyar ASUU ta tafi yajin-aiki, watanni tara kenan da rufe jami’o’in gwamnati. Kungiyar NLC ma ta yi barazanar zuwa yajin-aiki, amma daga baya ta fasa.
KU KARANTA: Lekki: Gwamnan Legas ya bayyana wanda su ka yi harbe-harbe
9. Karin farashin man fetur
A 2020 ne farashin man fetur ya yi tsadan da bai taba yi ba, gwamnatin tarayya ta kai kudin litar mai har zuwa N168-N172 a sakamakon janye tallafin man fetur da aka yi kwanaki.
10. Sauyin kudin lantarki
Wani babban labari a bana shi ne karin kudin wutar lantarki, wasu sun gamu da kusan karin 50%.
Tun watan Maris, abu yaci tura game da yajin-aikin ASUU. Ministan kwadago, Chris Ngige yace sai kungiyar malaman ta janye yajin-aiki, za a fito mata da kudinta.
Wankin hula ya kai gwamnati dare tun kungiyar ASUU ta ki janye dogon yajin-aikin da ta shafe watanni tara tana yi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng