Na hannun damar Buhari, Ismail Funtua, ya rasu

Na hannun damar Buhari, Ismail Funtua, ya rasu

Mallam Ismaila Isa Funtua, makusancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rasu a daren yau, Litinin, 20 ga watan Yuli. Mariga Funtua ne manajan darektan kamfanin jaridar 'Democrat' na farko, sannan ya taba rike shugaban kungiyar masu kamfanin jarida a Najeriya (NPAN).

Jaridar 'ThisDay' ta rawaito cewa Funtua ya mutu ne sakamakon ciwon zuciya.

Ita kuwa jaridar Daily Trust ta ruwaito kanin mamacin da aka sakaya sunansa, yana cewa: "Mallam ya shaidawa iyalansa cewa yana son ganin likitansa amma ya fara zuwa wajen mai yi masa aski.

"Shine ya tuka motar da kansa har zuwa asibiti bayan barin shagon mai askin," a cewar kanin.

Rahotanni sun bayyana cewa an ajiye gawar marigayin a masallacin Area 1, inda za a sallace shi a safiyar ranar Talata.

Ismaila Isah ya kasance mashahurin dan kasuwa, wanda ya mallaki ilimin gudanar da kasuwanci na sama da shekaru 30.

KARANTA WANNAN: Sa'ad Abubakar ya bukaci Musulmi su duba watan Dhul Hijjah daga gobe Talata

Ya taba kasancewa shugaban kamfanin sarrafa auduga na UNTL, wanda ya dauki ma'aikata sama da dubu goma aiki, kuma ya taba kasancewa ministan kasar Nigeria.

Na hannun damar Buhari, Ismail Funtua, ya rasu
Na hannun damar Buhari, Ismail Funtua, ya rasu Source: Twitter
Asali: Twitter

Shine wanda ya samar da kamfanin gine gine na Bulet International Nigeria Limited (kamfani mafi girma wanda 'yan asalin Nigeria ke tafiyar da shi), wanda kuma ya gina mafi yawan manyan gine ginen da ke cikin Abuja.

Har ya zuwa mutuwarsa, marigayi Funtua na daga cikin dattijai a kungiyar NPAN, sannan shine shugaban kamfanin gine - gine mai suna 'Bulet Construction Company'.

Za a yi jana'izarsa da safiyar ranar Talata bisa tsarin addinin Musulunci.

Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta na yanar gizo, Bashir Ahmad, ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan mamacin.

Ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel