Mahaifin Sulaiman ya gindaya wa Ba Amurkiyar data zo auren dansa sharudda guda 4

Mahaifin Sulaiman ya gindaya wa Ba Amurkiyar data zo auren dansa sharudda guda 4

Jeanine Delsky mata ce mai shekaru 45 'yar asalin kasar Amurka wacce ta sauka a Panshekara, wata anguwa a jihar Kano, don auren saurayinta mai shekaru 23 mai suna Suleiman Babayero Isa.

Delsky wacce ke rayuwa a California ta sauka a filin sauka da tashin jiragen sama ne na Aminu Kano a ranar Asabar kuma ta zarce har Panshekara don haduwa da iyayen masoyinta.

Masoyan sun hadu ne a shekarar da ta gabata a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram inda suka fara musayar hotuna da soyayya a yanar gizon.

Wasu majiyoyi kusa da dangin saurayin ta bayyana cewa za a yi auren ne watan Maris na wannan shekarar. Mtashin bakanon ya kammala karatunsa na sakadire ne kuma ya amince zai aure matar tare da bin ta zuwa Amurka.

Mahaifiyar Sulaiman, Malama Fatima ta ce bata da ta cewa a kan wannan hadin. Zata yi musu addu'ar zaman lafiya a yayin da suka koma Amurka.

A halin yanzu, mahaifin saurayin ya ce zai kai wa jami'an tsaron farin kaya rahoto don neman amincewarsu.

Malam Isa wanda tsohon dan sanda ne da ya kai matakin SP, ya samu zantawa da Kano Focus a gidansa da ke Panshekara. Ya bada sharudda hudu a kan auren.

DUBA WANNAN: Hisbah ta gayyaci 'yar Amurka data zo auren matashi a Kano, ta sha tambayoyi

Sharadi na farko shine samun yarjewar jami'an tsaro. "Muna kokarin samun yarjewar jami'an tsaro. A matsayina na tsohon dan sanda wanda ya yi murabus, zan garzaya ofishin DSS a ranar Litinin don sanar dasu halin da ake ciki."

Sharadi na biyu shine dansa zai ci gaba da karatunsa bayan sun isa Amurka sannan sharadi na uku shine Isa zai cigaba da addininsa na Islama ko bayan sun koma can. "Ina so yarona ya cigaba da karatu a can din kuma ya kiyaye addininsa na Islama." cewar tsohon dan sandan.

Tsohon dan sandan ya kara da cewa, "sai Jaenine Delsky ta kawo takardar yarjejeniyar tayi aure daga 'yan uwanta sannan za a a daura. Saboda addinin musulunci bai amince mace ta aurar da kanta ba."

Matar mai suna Jaenine Delsky zata koma kasarta ne nan da mako daya kuma zata dawo a watan Maris don bikin auren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel