Gwamnatin Tarayya ta fada wa Amurka, ba a tsangwamar addinan Jama’a

Gwamnatin Tarayya ta fada wa Amurka, ba a tsangwamar addinan Jama’a

- Kasar Amurka tana zargin Gwamnatin Najeriya da muzguna wa masu addini

- Ministan yada labarai yace kowa yana da ‘yancin ya zabi addininsa a Najeriya

- Lai Mohammed ya fitar da jawabi inda yayi wa gwamnatin Trump raddi a jiya

Gwamnatin tarayya ta musanya zargin da ake yi mata na cewa ta na hana Bayin Allah damar yin addinin da suka yi imani da shi a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto gwamnati tana kare kanta daga zargin da sakataren gwamnatin kasar Amurka, Mike Pompeo, ya jefe ta da shi jiya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Amurka raddi ne a ranar Talata, ta bakin Ministan yada labarai da al’adu na tarayya, Lai Mohammed.

Da yake magana a ranar 8 ga watan Disamba, 2020, Ministan kasar, yace abin da gwamnatin Amurkan take zargin Najeriya da shi ba daidai ba ne.

KU KARANTA: Yadda aka kama Maina a ofishin Jakadancin Amurka a Niamey

Mohammed ya fada wa gwamnatin Amurka cewa a Najeriya, kowa yana da damar ya bi ra’ayin da yake so, kuma ba tare da wani matsin-lamba ba.

Alhaji Lai Mohammed ya fitar da jawabi: “Najeriya ba ta dakile damar ‘yan kasa na yin addini, sannan kuma ba ta tsangwamar wasu masu addinai.”

Ya ce: “Wadanda suke fuskantar barazanar ta’addanci da rashin tsaro sun fito ne daga cikin mabiya addinin Musulunci, Kiristanci da sauran addinai.”

Duk da banbancin da aka samu, Mohammed ya ce gwamnatinsu zata cigaba da kokarin kare hakkin ‘yan kasarta na yin addinin da suka yi imani da shi.

KU KARANTA: Gwamnatin Shugaba Buhari za ta rage farashin litar man fetur

Gwamnatin Tarayya ta fada wa Amurka, ba a tsangwamar addinan Jama’a
Lai Mohammed Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Jawabin da Ministan ya yi daga birnin tarayya Abuja, ya zo ne jim kadan bayan sanarwar Amurka.

A ranar Litinin aka ji cewa gwamnatin Amurka ta sa Najeriya a cikin kasashe masu matsin lambar addini, inda ake tsangwamar jama'a saboda imaninsu.

Sauran kasashen da aka yi wa wannan shaida su ne: Burma, China, Eritrea, Iran, Nigeria, Koriya, Fakistan, Saudi Arabia, Tajikistan, da kuma Turkmenistan.

Wani Lauya a Abuja, Frank Tietie ya ji dadin matakin da Amurka ta dauka a kan Najeriya, ya ce an dade ana muzguna wa marasa rinjayen mabiya a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel