Oshiomhole ya bayyana abinda zai yi idan ya samu damar sake shugabancin APC

Oshiomhole ya bayyana abinda zai yi idan ya samu damar sake shugabancin APC

- Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya umarci lauyoyinsa da su janye korafin da ya kai kotu

- Oshiomhole ya ce ya amince da hukuncin da aka dauka a kansa na tube shi daga kujararsa, kuma ya gode da damar da aka bashi

- A cewarsa, bai rike wani wanda yayi sanadiyyar cire shi daga mukaminsa a ransa ba, kuma yana alfahari da nasarorin da aka samu a mulkinsa

Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar APC, ya ce idan aka bashi damar shugabantar jam'iyyar ba zai yi ba.

A ranar Litinin, Oshiomhole ya ce yana matukar alfahari da yadda NWC tayi aiki a karkashin mulkinsa, The Cable ta wallafa.

Oshiomhole ya ce bai riki kowa ba a zuciyarsa, har wadanda suka shiga suka fita har aka tumbuke shi daga mukaminsa ba, hasalima ya umarci lauyoyinsa da su janye korafin da ya tura a kan dakatar dashi da aka yi.

"Na umarci lauyoyina da su janye korafin da nayi a kan cireni da aka yi daga mukami na a matsayin shugaban jam'iyya," kamar yadda takardar tazo.

KU KARANTA: ASUU ta gindaya wa gwamnatin tarayya sabon sharadin komawa aiki

Oshiomhole ya bayyana abinda zai yi idan ya samu damar sake shugabancin APC
Oshiomhole ya bayyana abinda zai yi idan ya samu damar sake shugabancin APC. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Don haka, an gama yanke shawara aka cireni daga mukami na, kuma na amince da hukuncin dari bisa dari wanda aka yanke a kaina.

"Na riga na rufe wannan babin a rayuwata. Ko da kuwa NEC ta canja shawara, ko kuma kotu ta umarci a mayar da ni, zan ki amincewa da komawa kujerar shugaban jam'iyyar APC.

"Ina matukar alfahari da nasarorin da NWC ta samu a karkashin shugabancina, sannan na ji dadin yadda mambobi 18 suka taru, muka yi aiki duk don cigaban jam'iyya. Sannan kuma, ban rike wani wanda yayi sanadiyyar tubeni daga kujerata ba a rai na."

Oshiomhole ya mika godiyarsa ga shugaba Muhammadu Buhari saboda bashi hadin kai dari bisa dari lokacin yana shugabantar APC.

KU KARANTA: Buhari ya magantu a kan nasarar APC a zabukan maye gurbi

A wani labari na daban, tsohon sanatan Adamawa, Abdul'Aziz Nyako, da sauran mambobin ADC na Adamawa sun koma APC, jaridar Newswire ta wallafa.

Nyako ya sanar da manema labarai cewa, bayan shugabannin APC da na ADC sun tattauna, "Mun yanke shawarar yin maja da APC."

Wannan cigaban ya biyo bayan wani gagarumin taro da masu ruwa da tsakin jam'iyyar ADC da na APC suka yi a jihar Adamawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel