ASUU: Malaman Jami’ar Maiduguri sun koka a kan rashin biyan albashi

ASUU: Malaman Jami’ar Maiduguri sun koka a kan rashin biyan albashi

- Kungiyar ASUU ta UNIMAID ta ce an yi watanni biyar basu samu albashi ba

- ASUU ta ce Akawun gwamnati ya sabawa umarnin da Shugaba Buhari ya bada

- Wasu daga cikin malaman jami’ar tun Watan Fubrairu ba a biya su kudin su ba

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta reshen jami’ar tarayya da ke Maiduguri, ta fito ta koka a kan rashin biyan ‘ya‘yanta albashinsu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban kungiyar ASUU na bangaren UNIMAID, Farfesa Dani Mamman ya na korafi game da rashin albashin.

A wani jawabi da Dani Mamman ya fitar a madadin kungiyar malaman, ya ce akwai wadanda su ka kai tsawon watanni shida ba a biya su albashi ba.

“Wasu lamarin har ya kai tsawon watanni shida duk da umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada.” Inji Farfesa Mamman.

KU KARANTA: Farfesan Najeriya ya zama Shugaban Jami'a a Birtaniya

ASUU: Malaman Jami’ar Maiduguri sun koka a kan rashin biyan albashi
Babban akawun gwamnati
Asali: UGC

Shugaban na ASUU ya ce a cikin jami’o’in gwamnati 43 da ke Najeriya, an biya dukkaninsu bashin albashinsu face UNIMAID da wata jami’a guda.

Malaman jami’ar sun zargi babban Akawun gwamnatin tarayya da laifi, ASUU ta ce Akawun bai bi umarnin da aka bada na biyan kowa kudinsa ba.

Kungiyar ta ASUU ta yi kira ga gwamnati ta tabbatar cewa an biya kowane malamin makarantar UNIMAID kudinsa ba tare da an sake samun jinkiri ba.

Dayan jami’ar da har yau ba a biya malamanta ba ita ce jami’ar koyon aikin gona ta Michael Opara, da ke garin Umudike, Abia.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng