Buhari ba zai yi murubas ba don kallubalen tsaro, martanin APC ga PDP

Buhari ba zai yi murubas ba don kallubalen tsaro, martanin APC ga PDP

- Kwamitin zartarwar jam'iyyar APC ya yi Allah-wadai da kiran da jam'iyyar PDP ke yi ga shugaban kasa da yayi murabus

- Kwamitin ta bakin El-Rufai gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa yanzu ba lokacin siyasantar da batun matsalar tsaro ba ne

- Kwamitin ya kuma bayyana cewa hanya daya da za a bi shi ne a cire bambancin siyasa

Kwamitin zartarwar jam'iyyar APC ya yi watsi da kiran da jam'iyyar PDP ta yi na cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar nan.

A baya bayan nan ne PDP ta yi kira ga shugaban kasa da ya yi murabus saboda matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

Buhari ba zai yi murubas ba don kallubalen tsaro, martanin APC ga PDP
Buhari ba zai yi murubas ba don kallubalen tsaro, martanin APC ga PDP. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Budurwa ta yi karar saurayinta bayan shafe shekara 8 suna soyayya ba amma ya ƙi aurenta

Amma kwamitin zartarwar jam'iyyar APC ya ce shugaban ba zai yi murabus ba.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, shi ne ya bayyana haka bayan kammala taron kwamitin ranar Talata a Abuja, ya ce sun yi Allah wadai da kiraye kirayen "da kakkausar murya".

Ya ce kwamitin zartarwar APC ya fusata kan yadda aka maida sha'anin tsaro ya zama siyasa wanda jam'iyyar adawa ke yi don cimma bukatun siyasa.

Ya ce, "kwamitin cikin kakkausar murya, ya yi Allah wadai da kiran da shugabancin PDP da wasu manyan su ke yi kan shugaban kasa ya yi murabus.

KU KARANTA: Labari mai zafi: Buhari ya sallami shugaban Hukumar NDE, Ladan Argungun

"Kwamitin ya bayyana cewa matsalolin tsaro, masu ban takaici, za a iya kawo karshen su ne kadai idan an hado kan manufa guda, farar hula da jami'an tsaro, gwamnati da yan adawa da kowane dan kasa su hadu ba tare da bambancin jam'iyyar siyasa ba.

"Wannan ba lokacin maida matsalar tsaro siyasa bane."

A wani labrin daban, kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki a ranar Talata ya janye sharadin takara ga wanda suka shiga ko suke shirin shiga jam'iyyar.

Sharadin zai bada damar tsayawa takara a duk wata kujerar mulki ba tare da la'akari da dadewa a jam'iyyar ba.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka ga majalisa bayan kammala taron kwamitin kamar yada The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel