Budurwa ta yi karar saurayinta bayan shafe shekara 8 suna soyayya amma ya ƙi aurenta

Budurwa ta yi karar saurayinta bayan shafe shekara 8 suna soyayya amma ya ƙi aurenta

- Gertrude Ngoma ta bayyanawa kotu cewa ta gaji da jiran auren Herbert Salaliki

- Ngoma ta na zaune da iyayen ta duk da cewa tana da ɗa tare da Herbert wanda shi zaman kansa ya ke.

- Budurwar ta ce ta yi tantamar imanin Herbert bayan ta gano cewa ya na aikewa wata budurwar sako

Wata budurwa ta yi karar saurayin ta sakamakon bata bata mata lokaci ba tare da auren ta ba kuma suna tare tsawon shekara takwas.

Gertrude Ngoma mai shekaru 26 ta shaidawa kotu a Zambia cewa ta gaji da jiran Herbert Salaliki mai shekara 28, wanda yayi alkawarin auren ta.

Budurwa ta yi karar saurayinta bayan shafe shekara 8 suna soyayya ba amma ya ƙi aurenta
Budurwa ta yi karar saurayinta bayan shafe shekara 8 suna soyayya ba amma ya ƙi aurenta. Hoto: Mwebantu
Asali: Twitter

A wani rahoto, Ngoma ta na zaune a gaban iyayen ta duk da cewa ta haihu tare da Herbert wanda yake zaman kansa.

DUBA WANNAN: Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu

An ruwaito cewa tuni saurayin ya biya sadakin amma har yanzu bai auri budurwar ta sa ba.

Ta ce: "bai maida hankali ba, shi yasa na kawo shi kotu saboda ina so in san makomar mu".

Ngoma ta ce ta yi tantamar imanin Herbert bayan da ta gano ya na aikawa wata budurwar sako wadda ta ke zargi akwai wani abu tsakanin ta da saurayin na ta.

Da ya ke kare kansa, Herbert ya ce har yanzu ba shi da kudin da za su isa aure kuma ya zargi Ngoma da rashin fahimtar sa.

KU KARANTA: A rataye ni a tsakiyar kasuwa har in mutu, in ji wanda ake zargi da garkuwa a Kano

Alkalin da ke sauraren karar ya shawarce su da su yi sulhu kasancewar ba maganar wani yayi aure a cikin su.

A wani labrin daban, kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki a ranar Talata ya janye sharadin takara ga wanda suka shiga ko suke shirin shiga jam'iyyar.

Sharadin zai bada damar tsayawa takara a duk wata kujerar mulki ba tare da la'akari da dadewa a jam'iyyar ba.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka ga majalisa bayan kammala taron kwamitin kamar yada The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel