'Yan daba sun kaiwa basarake hari, sun lalata masa fada

'Yan daba sun kaiwa basarake hari, sun lalata masa fada

- Wasu da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun kai fari fadar basaraken Ode, Oba Sunday Boboye a jihar Ondo

- Rahotanni sun bayyana cewa harin ba zai rasa nasaba da rikicin fili da ake yi ba tsakanin garin Ode da Isinigbo

- Oba Sunday Boboye ya yi kira ga 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan harin da yace shi aka kai wa

Wasu 'yan daba a ranar Talata sun kai wa basaraken garin Ode, Oba Sunday Boboye hari a fadarsa da ke Ode, karamar hukumar Akure ta Arewa suka lalata kayayyaki.

Wannan shine karo na biyu da 'yan daban ke kai hari a fadansa cikin mako guda inda har suka yi kone-kone a baya.

Bayan harin, Oba Boboye ya tashi daga fadar ya koma fadarsa ta biyu inda nan ma yanzu suka biyo shi suka masa barna a ranar Talata.

'Yan daba sun kaiwa basarake hari, sun lalata masa fada
'Yan daba sun kaiwa basarake hari, sun lalata masa fada. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

The Punch ta ruwaito cewa harin ba zai rasa nasaba ba da rikicin fili da ke yi tsakanin garin Ode da makwabtansu na garin Isinigbo.

DUBA WANNAN: Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu

A cewar wani ganau, yan daban sun afka garin ne misalin karfe 12.05 na daren ranar Talata suna ta harbi yayin da mutane ke barci.

Bayan nan sai suka nufi fadar sarkin suka cigaba da harbe-harben.

A martanin da ya yi, basaraken yace an kai harin ne domin ayi masa lahani.

Ya ce, "Ina son IGP na 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro suyi bincike. Wannan babu shakka an zo ne don a kona min gida, ayi min barazana da kuma yunkurin halaka ni da ni da iyalai na."

KU KARANTA: Budurwa ta yi karar saurayinta bayan shafe shekara 8 suna soyayya ba amma ya ƙi aurenta

Kakakin 'yan sandan jihar, Mista Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce sun tura jami'ai zuwa unguwar don kwantar da tarzomar.

Ya kara da cewa an fara bincike a kan lamarin.

A wani labrin daban, kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki a ranar Talata ya janye sharadin takara ga wanda suka shiga ko suke shirin shiga jam'iyyar.

Sharadin zai bada damar tsayawa takara a duk wata kujerar mulki ba tare da la'akari da dadewa a jam'iyyar ba. 2023: Jam'iyyar APC ta sahalewa Umahi, Dogara da wasu tsayawa takara.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka ga majalisa bayan kammala taron kwamitin kamar yada The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel