Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu

Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu

- Dan shugaban jam'iyyar APC reshen Jihar Nasarawa da 'yan bindiga suka kashe ya bayyana abubuwan da suka faru yayin da aka kai musu hari

- Samuel Shekwo ya ce 'yan bindigan sun yi wa gidansu kawanya suka rika harbi har sai da suka shigo sannan suka gano mahaifinsa a cikin bandaki

- Ya ce 'yan bindigan sun musu alkawarin cewa ba za su kashe shi ba kawai kudi suke so don a cewarsu ba shi kadai zai ci kudin gwamnati ba

Samuel Shekwo, dan gidan shugaban jam'iyyar APC na Nasarawa da aka kashe, ya bayyana yadda yan bindiga suka shigo gidansu har suka gano mahaifinsa a maboyarsa.

A satin da ya gabata ne wasu mutane dauke da makamai suka yi garkuwa da marigayin a Lafia, babban birnin jihar, waccan Asabar din.

Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu
Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Yan bindigar sun yi musayar wuta da jami'an tsaro da ke tsaron lafiyar shugaban APCn kafin su yi awon gaba da shi kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Daga bisani kuma jami'an yan sanda suka tsinci gawar sa ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: Mutanen gari sun kashe dan bindiga da duka a Katsina

A hirar da yayi da jaridar The Nation, dan marigayin ya yi bayanin yadda masu garkuwar suka gano inda mahaifin sa ya buya a bandaki.

A cewar sa, yan bindigar sun yi yunkurin tafiya da shi a maimakon mahaifinsa bayan binciks gidan da farko ba tare da sun ga baban na shi ba.

Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu
Yadda makasan mahaifina suka gano inda ya boye, dan shugaban APC da aka kashe ya magantu. Hoto @thecableng
Asali: Twitter

"Da daren Asabar, duk muna gida. Baba ya je ya busa wasan 'golf' ya kuma dawo da misalin karfe 8:00 na dare, kuma na je daki na gaishe shi. Ya gama cin abinci ya na kuma bani labarin yadda wasa ya kasance sai na fice daga dakin na barshi da sauran mutane suna kallon talabijin," a cewar sa.

"Mintuna kadan kafin 10:00 na dare, daya daga cikin abokan karatu na a jami'ar jihar Nasarawa ya kira ni a waya muna tattauna batun yajin aiki. Kawai ban tsammani sai na fara jin harbe harbe ta ko ina a fadin gidan.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: 'Yan Boko Haram sun yi wa manoman shinkafa 44 yankan rago a Borno

"Na ajiye wayar ba tare da ko gintse kiran ba kuma na fice daga dakina. Sai na fara duba dakin iyayena don duba lafiyar su, sai na hangi baba na zai fita daga daki. Sai na kashe hasken dakin saboda kada a ganmu saboda na kula maharan sun zagaye mu," in ji Shekwo.

Shekwo ya cigaba da cewa 'yan bindigan sun yi wa gidansu kawanya suna ta harbe-harbe har sai da suka balle kofar gidan suka shigo suka yi bincike amma basu ga mahaifinsa ba. Hakan yasa suka yi niyyar tafiya da shi.

Sai dai kafinsu tafi daya daga cikinsu ya lura wani daki a rufe yake, daga nan ya balle dakin bai ga kowa ba sai ya lura bandaki na rufe. Ya ce, "sun gaza bude kofar bandakin don mahaifina ya tare kofar amma sai suka yi barazanar yin harbi daga nan ne ya bude kofar."

Daga nan ne suka tafi da mahaifina duk da rokon da muka musu inda suka ce ba zasu kashe shi ba domin kudi kawai suke so. Daga bisani kawai sai muka ji labarin an gano gawarsa.

A wani labarin daban, kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel