Yadda Boko Haram suke amfani da fasahar Intanet wurin watsa bidiyoyi

Yadda Boko Haram suke amfani da fasahar Intanet wurin watsa bidiyoyi

- Barista Bukarti ya ce 'yan Boko Haram suna amfani da dabaru na musamman

- A cewarsa, bincikensa ya nuna cewa inda Shekau yake, babu intanet

- Kuma yana daukar bidiyon a inda yake, sai ya baiwa mabiyansa su yada

Barista Bukarti ya ce bincikensa ya gano cewa shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau yana zaune ne a wurin da bubu intanet.

A yadda Bukarti yace, "Idan Shekau yayi bidiyo dauke da bayanansa a wurin da yake, wakilansa ne suke da alhakin gyara bidiyon su watsa wa duniya. 'Yan Boko Haram suna zuwa wuraren Maiduguri ne don samun intanet."

Bukarti ya kara da cewa, akwai lokacin da bincikensa ya gano cewa idan sun nadi bayanai kuma suna bukatar watsa wa a duniya suna shan wahala kwarai wurin neman intanet, BBC ta wallafa.

Yadda Boko Haram suke amfani da fasahar Intanet wurin watsa bidiyoyi
Yadda Boko Haram suke amfani da fasahar Intanet wurin watsa bidiyoyi. Hoto daga metro.co.uk
Source: Facebook

Ya ce mayakan Boko Haram suna da dabaru daban-daban, don ba da ka suke aiwatar da ta'addancinsu ba. Tabbas sunada masana ilimin kwamfuta a cikinsu.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Hoton Buratai yana kwasar nishadi yayin buga kwallon 'Golf' ya janyo cece-kuce

Ya kara da cewa, "Suna yin karance-karance a kan yadda za su yada sakonninsu ba tare da kowa ya gane ba. A cikin lambobin da suke amfani dasu ta WhatsApp za a ga wasu lambobin na Sudan ko Nijar ne, har da ta Libiya.

"Wadannan dabarun suke hanawa a gano su, kuma basa yin waya, sun fi amfani da WhatsApp saboda yafi tsaro."

Akwai 'yan kungiyar daga Mali, Burkina Faso da sauran kasashe. Idan ba a manta ba, sun taba kai hare-harensu Mali da Burkina Faso, inda suka ce sun fadada cibiyoyinsu a yankin kudu da Hamadar Sahara.

KU KARANTA: Kyau da kwakwalwa: Hotunan sarakunan gargajiya mata 7 a Najeriya

"Sannan hotuna da bidiyoyin hare-harensu suna rarrabawa ne a zaurukansu na WhatsApp da suka bude. Akwai 'yan kungiyar da ke Najeriya, Iraki da Syria, wadanda suke rarraba sakonninsu," kamar yadda mai binciken yace.

A wani labari na daban, Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, ya ce ya yi wuri shugabannin APC su fara magana a kan zaben shugaban kasa na 2023.

Ya fadi hakan ne a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba yayin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC.

Kashim ya bayyana hakan, inda yace ana karkatar da hankulan shugabanni a kan abubuwan da ke faruwa a kasa a halin yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel