Da yawan almajiran da ke tituna ba 'yan Najeriya bane, Gwamna Ganduje

Da yawan almajiran da ke tituna ba 'yan Najeriya bane, Gwamna Ganduje

- Gwamnan jihar Kano, Abdulllahi Umar Ganduje ya bayyana cewa almajiran da ke Najeriya ba 'yan kasa bane

- Kamar yadda ya sanar, ya ce da yawansu da ke yawo a tituna 'yan kasashen Nijar, Chadi da Kamaru ne

- Ya tabbatar da cewa kawo tsarin Boko a lamarin almajiranci zai matukar kawo cigaba a fannin ilimi

Da yawa daga cikin daliban makarantun allo, wadanda aka fi sani da Almajirai, wadanda ke yawo a titunan arewacin kasar nan ba 'yan Najeriya bane a cewar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

"Da yawansu daga kasashen ketare suke kamar jamhuriyar Nijar, Chadi da Kamaru," Ganduje yace yayin bude taron kwanaki uku da UBEC take a jihar Kano.

"Daga binciken da muka yi, da yawa daga cikin almajiran da ke yawo a titunanmu daga kasashen Nijar, Cahdi da Kamaru suke.

KU KARANTA: Kyau da kwakwalwa: Hotunan sarakunan gargajiya mata 7 a Najeriya

Da yawan almajiran da ke tituna ba 'yan Najeriya bane, Gwamna Ganduje
Da yawan almajiran da ke tituna ba 'yan Najeriya bane, Gwamna Ganduje. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

"Matukar aka inganta yanayin karatun Almajiri, za a janyo almajiran ne daga sauran jihohin. Wannan kuwa ba matsala bane.

“Gwamonin arewa suna matsawa wurin samar da dokar da za ta hana lmlajirai shiga wata jiha daga ta su," yace.

Ganduje ya bayyana cewa, karatun firamare da na sakandare zai zama kyauta kuma dole, hakan ne kadai hanyar gyara tsarin almajiranci inda za a bai wa bangaren ilimi fifiko, Daily Nigerian ta wallafa.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Hoton Buratai yana kwasar nishadi yayin buga kwallon 'Golf' ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, jam'iyyar APC ta kara samun tabbacin cewa har yanzu 'yan Najeriya ita suke yayi, bayan ganin dumbin nasarorin da ta samu a zaben maye gurbi da aka yi, kamar yadda fadar shugaban kasa tace.

Malam Garba Shehu, babban hadimin shugaba Muhammadu Buhari a kan harkar yada labarai ya sanar da hakan.

A wata takarda da ya saki a Abuja ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, kakakin shugaban kasa yace hakika Shugaba Muhammadu Buhari ya yi matukar farinciki da jin nasarorin da APC ta samu a zaben maye gurbin da aka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel