A rataye ni a tsakiyar kasuwa har in mutu, in ji wanda ake zargi da garkuwa a Kano

A rataye ni a tsakiyar kasuwa har in mutu, in ji wanda ake zargi da garkuwa a Kano

- Wani matashi da ake zargi da kashe wani yaro mai shekaru 16 a Kano ya roki a rataye shi a bainar jama'a har sai ya mutu

- Matashin ya yi garkuwa da yaron kuma ya bukaci mahaifin yaron ya biya shi naira miliyan 1.3 kudin fansa amma duk da haka ya kashe yaron

- Rundunar 'yan sandan jihar ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar ta kammala bincike a kansa

Wani da ake zargi da garkuwa da mutane ya roki a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataye shi saboda garkuwa da wani Tijjani Kabiru, kashe shi sannan ya birne shi a kabari mara zurfi.

Anass mai shekaru 22 ya yi garkuwa da Kabiru mai shekaru 16 a ranar 9 ga watan Janairu a Kwanar Gwarmai a garin Kwantagora da ke Karamar hukumar Bebeji na Jihar Kano a cewar 'yan sanda.

An gano cewar ya bukaci a biya shi kudin fansa har naira miliyan 1.3 da kuma katin waya na N20,000 daga mahaifin yaron, Alhaji Kabiru.

A rataye ni a tsakiyar kasuwa har in mutu, in ji wanda ake zargi da garkuwa
A rataye ni a tsakiyar kasuwa har in mutu, in ji wanda ake zargi da garkuwa. Hoto @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama

Sai dai ya kashe wanda ya yi garkuwar da shi kafin a biya shi kudin fansar kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, wanda ake zargin ya ce ya kashe wanda ya yi garkuwar da shi ne don ya rasa inda zai boye shi.

Wanda ake zargin, a ranar Juma'a, ta jagoranci tawagar 'yan sanda da likitoci zuwa wani gona a daji inda ya shake shi ya kashe shi sannan ya birne shi.

An ciro gawar mammacin don bincike sannan ayi jana'iza.

Wanda ake zargin ya ce ya aikata mummunar aika-aikan ne bayan ya yi tatil da kwayoyi da ganyen wiwi.

KU KARANTA: Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Hotuna)

Cikin nadama kan abinda ya aikata, ya roki a rataye shi har sai ya mutu a tsakiyar kasuwa don ya zama darasi ga wasu da ke niyyar yin garkuwa da mutane.

"Ban taba aikata irin wannan mummunar abin ba; ba aiki na bane. Roko na ga gwamnati da kowa shine a yanke min hukuncin kisa ta hanyar rataya a bainar jama'a," in ji shi.

Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna, ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu idan an kammala bincike.

A wani labarin daban, kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel