Sojoji sun kashe yan bindiga uku a Binuwai

Sojoji sun kashe yan bindiga uku a Binuwai

- Rundunar soji ta 'Operation Whirl Stroke (OPWS) ta hallaka mutane uku a wani barin wuta da suka yi a daren Lahadi

- An ruwaito cewa yan bindigar sun mamaye Adaka kuma suna yi wa mutanen yankin fashi

- Mazauna yankin sun bayyana cewa ba don sojoji sun kawo musu dauki ba, da abin ya munana

Rundunar soji ta musamman ta 'Operation Whirl Stroke' (OPWS) ta hallaka mutane uku da ake zargin 'yan bindiga ne a wani barin wuta da daren Lahadi da ya faru a yankin Adaka da ke Makurdi a jihar Benue.

Wasu daga cikin mutanen yankin, sun bayyanawa jaridar Daily Trust cewa 'yan bindigar sun mamaye Adaka, wata unguwa a cikin garin Makurdi kuma suna yi wa mazauna yankin fashi kafin sojoji su ceto su.

An ruwaito cewa sojojin sun samu kira daga mazauna yankin lokacin da suke sintiri a yankin don kawar da yan bindigar, an yi barin wutar da yayi sanadiyar mutuwar mutane uku da ake zargin.

Sojoji sun kashe yan bindiga uku a Binuwai
Sojoji sun kashe yan bindiga uku a Binuwai. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: A rataye ni a tsakiyar kasuwa har in mutu, in ji wanda ake zargi da garkuwa a Kano

Mazauna yankin sun fadawa manema labarai a Makurdi cewa lamarin ya faru da misalin karfe 8:00 na dare, kuma ba don sojoji sun yi gaggawar kawo musu dauki ba da abin ya kazanta tunda har ana zargin 'yan bindigar sun harbi wasu ma'aurata.

Da aka tuntubi babban kwamandan OPWS, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya tabbatar wa manema labarai cewa tawagar sintirinsa sun yi bata-kashi tsakanin su da 'yan bindiga a Adaka.

"Jami'an mu a shirye suke kuma za su yi duk mai yiwuwa tare da sauran jami'an tsaro don kare al'umma," a cewarsa.

KU KARANTA: Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Hotuna)

Yekini ya kuma shaidawa manema labarai da su tuntubi mai magana da yawun hedikwatar tsaro don jin karin bayani a kan batun.

A wani labari na daban, 'yan sandan Jihar Katsina a ranar Asabar sun tabbatar da mutuwar wani da ake zargi dan bindiga ne a karamar hukumar Malumfashi da ke jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Gambo Isah, ya ce yan bindiga kusan guda uku, da misalin 1:30 na daren Asabar, sun kai hari gidan wani mutum, Hari Bello, sun kuma jikkata yara biyu.

Jami'an sun ce wanda aka kaiwa harin sun yi kuwwa, wanda hakan ya ja hankalin makwabta da yan sanda. Saboda haka an kora yan bindigar kuma an ci gaba da bin su. An tarar da daya daga cikin yan bindigar kuma fusatattun mutanen suka rufe da duka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel