A cikin sa'o'i 6, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Benin kuma ta koma Legas a babur
- Wata jarumar 'yar Najeriya, Fehintoluwa, ta yi tafiya daga Legas zuwa Benin a babur, kuma ta koma cikin sa'o'i 6
- Budurwar ta ce bata sanar wa kowa ba, saboda bata so a hanata aiwatar da abinda tayi kudirin aikatawa
- Bayan Fehintoluwa ta je ta koma, ta wallafa hotunanta wadanda ta dauka a kan hanyar ta, a shafinta na Twitter
Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Fehintoluwa Okegbenle, ta bayyana tafiya mai nisa da tayi a kan babur, a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.
Mutane da dama sun yi ta yaba wa wannan bajintar da tayi. Ta yi wallafar ne a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, Fehintoluwa ta ce ta kama wannan doguwar tafiyar ne, tun daga jihar Legas zuwa Benin.
A cewarta, sa'o'i 6 ta dauka a kan babur, daga tashinta har zuwa da komawarta cikin Legas. Idan ba a manta ba, wannan budurwar ta taba zuwa tun daga Legas zuwa Abuja a kan babur, cikin sa'o'i 13.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi barazanar lalata da diyarmu idan bamu kai kudi ba, Iyayen budurwa
Ta ce ba ta taba auna karfi da kuzarinta ba kamar na ranar, duk da dai mutane da dama sun yi ta kokarin dakatar da ita, amma ta jajirce.
Wannan karon kuwa, bata yi shawara da kowa ba, ta kama hanya ta tafi.
A cewar Fehintoluwa, bata taba tafiya mai ban sha'awa da ta kai wannan ba. Bayan kammala wannan tafiyar ne ta wallafa a shafinta na Twitter, wanda hakan ya janyo fiye da mutane 13,000 suna yaba mata, sannan fiye da mutane 2,000 suka yada wallafar ta ta.
Sannan jama'a da dama sun yi ta tsokaci. Wani Chrysmekus cewa yayi: "Barka, gaskiya kin yi sauri sosai. Ni kaina ina fatan idan na siya nawa babur din zan gwada makamancin hakan. Ina so in kewaye kasar nan, inje Porthacourt zuwa Maiduguri, Maiduguri zuwa Legas, Legas zuwa Taraba. Daga nan sai in koma Abuja. Ba a lokaci guda ba, kila ko sau daya a shekara."
Wata Mekkah_medina ta ce: "Sak lokacin da nayi amfani da shi a mota, daga Lagos Island zuwa Alagbado, duk cikin jihar Legas, a kan titi daya."
Wata Nwaneri_Richard ya ce: "Ina ga zan siya irin wannan babur din, don yanzu haka na kasa tara kudin mota."
KU KARANTA: Da duminsa: Sojin Najeriya sun bankado wani harin 'yan bindiga a Kaduna
A wani labari na daban, CCB za ta gabatar da Magu, tsohon shugaban EFCC gaban CCT, daga yanzu zuwa kowanne lokaci, kamar yadda TheCable ta fahimta.
Kamar yadda labarai suka bayyana, za a yanke wa Magu hukunci saboda kin ambaton wani asusun bankinsa yayin cike takardar bayyana kadarori.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng