Yadda 'yan bindiga suka fatattake mu har zuwa Nijar, Manoman Sokoto

Yadda 'yan bindiga suka fatattake mu har zuwa Nijar, Manoman Sokoto

- Mazauna Gudu da ke karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto, sun koka a kan rashin tsaro

- Sun ce 'yan bindiga sun addabesu, har ta kai ga basu iya kwana a gidajensu saboda bala'i

- Sun ce suna tserewa kasar Nijar, su koma gidajensu washegari don gudun a yi garkuwa dasu

Mazauna kananun hukumomin Gudu da Tangaza da ke jihar Sokoto, sun koka a kan yadda al'amuran 'yan bindiga suka takura su har suke kai ga neman wurin rabewa a kasar Nijar.

A cewarsu, 'yan bindiga suna zuwa garuruwansu da yamma, su amshe dukiyoyi masu tarin yawa daga hannayen masu hali a cikinsu, ko kuma su yi garkuwa da su.

Daya daga cikin mazauna kauyen Kurdula, ya bayyana wa BBC cewa da yawansu suna tserewa kasar Nijar da yamma sai su koma gidajensu da safe.

KU KARANTA: Hotunan angon da sheka lahira sa'o'i kadan bayan daurin aurensa

Yadda 'yan bindiga suka fatattake mu har zuwa Nijar, Manoman Sokoto
Yadda 'yan bindiga suka fatattake mu har zuwa Nijar, Manoman Sokoto. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun samo miyagun makamai a Benue (Hotuna)

Kamar yadda ya bukaci a boye sunansa, yace "Al'amarin ya kazanta a kananun hukumomin Gudu da Tangaza.

"Duk dare, 'yan bindiga suna zuwa kauyakunmu da bindigogi, sai su yi ta zagayen gidaje. Idan ka nuna musu baka da kudi, sai su tilasta maka nuna musu gidan mai kudi don su yi garkuwa da shi.

"Ko a ranar Lahadi, sun yi garkuwa da mutane 2, kuma har yanzu basu sako su ba, saboda basu riga sun biya su kudaden fansa ba."

Kwamishinan tsaro na jihar, Garba Moi Isa, ya bayyana wa BBC cewa gwamnatin jihar tana samun nasarori wurin yaki da ta'addanci.

A wani labari na daban, wani Promise David mai shekaru 27 yayi wa karuwarsa, Esther Pascal, mai shekaru 18 dukan kawo wuka har ta kai ga mutuwa sakamakon fada a kan abinci da kudin kulawa da diyarsa.

Al'amarin ya faru ne a ranar Lahadi da tsakar dare a layin Ebis Machanic, Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Marigayiyar ta haifa wa mutumin mai aiki a wani wurin wanke mota, yarinya wacce yanzu shekarunta 2 da haihuwa, The Nation ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel