Tsohon sanatan Adamawa, Nyako, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Tsohon sanatan Adamawa, Abdul'Aziz Nyako, da sauran 'yan jam'iyyar ADC na jihar sun koma APC
- A cewarsa, sun lura da yadda jam'iyyar APC take tafiyar da lamurranta cikin kwanciyar hankali
- Ya ce sai da suka tattauna da masu ruwa da tsakin jam'iyyar tukunna suka yanke wannan shawarar
Tsohon sanatan Adamawa, Abdul'Aziz Nyako, da sauran mambobin ADC na Adamawa sun koma APC, jaridar Newswire ta wallafa.
Nyako ya sanar da manema labarai cewa, bayan shugabannin APC da na ADC sun tattauna, "Mun yanke shawarar yin maja da APC."
Wannan cigaban ya biyo bayan wani gagarumin taro da masu ruwa da tsakin jam'iyyar ADC da na APC suka yi a jihar Adamawa.
"Mun ga yanayin jajircewa da dagewa wurin yin shugabancin APC, sai muka yanke shawarar angulu ta koma gidanta na tsamiya, wato mu koma APC.
KU KARANTA: Bidiyon COS na gwamna yana watsa wa fasto kudi a ofishinsa ya janyo cece-kuce
"Shugabannin jam'iyyar ADC za su tattauna a kan wannan majar ga hedkwatar jam'iyyar ta kasa, don yin mai yuwuwa," a cewarsa.
Nyako, wanda yazo a matsayi na 3 a zaben sanatocin ya bayar da tabbacin cewa sun bai wa jam'iyyar PDP ta jihar Adamawa damar tafiyar da mulkinta cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma sun gane cewa sun fi dagewa wurin siyasa a kan mulki.
KU KARANTA: Rashin tsaro: Hoton Buratai yana kwasar nishadi yayin buga kwallon 'Golf' ya janyo cece-kuce
"Sun samar da siyasa mara karfi ta yadda karamar iska ta isa ta zubar da jam'iyyar, don haka mun dawo APC, sannan kwanan nan za mu haska a jihar Adamawa," a cewarsa.
A wani labari na daban, jam'iyyar APC ta kara samun tabbacin cewa har yanzu 'yan Najeriya ita suke yayi, bayan ganin dumbin nasarorin da ta samu a zaben maye gurbi da aka yi, kamar yadda fadar shugaban kasa tace.
Malam Garba Shehu, babban hadimin shugaba Muhammadu Buhari a kan harkar yada labarai ya sanar da hakan.
A wata takarda da ya saki a Abuja ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, kakakin shugaban kasa yace hakika Shugaba Muhammadu Buhari ya yi matukar farinciki da jin nasarorin da APC ta samu a zaben maye gurbin da aka yi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng