Gwamnati ta kaddamar da shirin MSME na taimakon Direbobi inji Yemi Osinbajo

Gwamnati ta kaddamar da shirin MSME na taimakon Direbobi inji Yemi Osinbajo

- Ana cigaba da raba kudin tallafin MSME ga wadanda suka shiga matsin tattali

- Gwamnatin Tarayya tace zata waiwayi Direbobin motoci da 'Yan Keke Napep

- Yemi Osinbajo yace an fara shirin raba wa ‘Yan acaba da ‘Yan dako N30, 000

Mun ji cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin tallafa wa wasu rukunin marasa karfi a karkashin tsarin MSME Survival Fund da aka kawo.

Daily Trust ta rahoto Mai magana da yawun bakin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, yana cewa za a tallafa wa direbobi da masu tura-baro.

Mista Laolu Akande ya fitar da jawabi jiya, yace gwamnati za ta taimaka wa ‘yan dako da direbobi a yunkurin da ta ke yi na ceto kananan ‘yan kasuwa.

KU KARANTA: Abin da Osinbajo ya fada game da rashin tsaro a 2015

Gwamnatin tarayya na kokarin ganin ta rage radadin da jama’a suka shiga a sakamakon annobar COVID-19 wanda ya lahanta tattalin arzikin kasashe.

Akande yace kofa a bude take na wannan tallafi har zuwa ranar Litinin, an fara kaddamar da wannan tsari ne a ranar 1 ga watan Oktoban da ta wuce.

“Yayin da masu sana’ar hannu suka fara karbar gudumuwar N30, 000 dinsu, ‘Yan Najeriya dake harkar sufuri – motoci, cata, bas, keke napep, acaba, ‘yan dako da sauransu suna da damar cin moriyar wannan shiri a yanzu.” Inji Laolu Akande.

Masu sana’a 59, 000 aka aika wa N30, 000 domin a farfado da su inji hadimin fadar shugaban kasar.

KU KARANTA: Ba takara ke gaba na ba - Osinbajo

Gwamnati ta kaddamar da shirin MSME na taimakon Direbobi inji Yemi Osinbajo
Yemi Osinbajo yana jawabi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

An biya wadannan mutane ne a jihohi 24 da Abuja: Legas, Ekiti, Kaduna, Borno, Kano, Bauchi, Anambra, Abia, Ribas, Filato, Delta, Taraba, Adamawa, Bayelsa, Edo, Ogun, Ondo, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Enugu, da Ebonyi.

Jihohin da ba a fara rabon ba sune: Akwa-Ibom, K/Riba, Zamfara, Yobe, Sokoto, Nasarawa, Niger, Imo, Oyo, Osun, Jigawa, Gombe and Benuwai.

A makon da ya gabata ne ku ka ji mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, yana cewa Najeriya tana da dinbin arziki a Duniya.

Osinbajo ya ce kasar nan ta tara duk wani abu da kowace kasa take nema don ta daukaka.

Mai girma Farfesa Yemi Osinbajo ya fadi hakane a ranar Talatar da ta wuce a wajen wani taro na NASIDRC da aka yi a Lafia, jihar Nasarawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng