Bidiyon COS na gwamna yana watsa wa fasto kudi a ofishinsa ya janyo cece-kuce

Bidiyon COS na gwamna yana watsa wa fasto kudi a ofishinsa ya janyo cece-kuce

- Bidiyo shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Abia ya janyo cece-kuce

- A bidiyon mai tsawon dakika 27, an ga Anthony Agbazuere yana watsa wa wani fitaccen fasto kudi

- An gansu a cikin ofishin shugaban ma'aikatan gwamnan jihar yana watsa masa kudi yayin da yake addu'o'i

Wani bidyo da yake nuna shugaban ma'aikatan fadar gwamna jihar Abia, Anthony Agbazuere yana zuba wa wani fasto mai suna Odumeje wanda aka fi sani da Indaboski ya janyo cece-kuce.

A bidyon da wani mai suna Enwagboso ya wallafa a shafinsa na Twitter, an ga Agbazuere yana watsa wa Chuwuemka Ohanaremere wanda aka fi sani da Odumeje kudi.

A bidiyon, ba a ga wacce rana lamarin ya faru ba, amma ya bayyana cewa a ofishin Agbazuerre ya faru, Channels Tv ta wallafa.

KU KARANTA: Bidiyon soja yana dukan budurwa tare da yi mata tsirara a titi kan shigar banza

Bidiyon CSOn gwamna yana watsa wa fasto kudi a ofishinsa ya janyo cece-kuce
Bidiyon CSOn gwamna yana watsa wa fasto kudi a ofishinsa ya janyo cece-kuce. Hoto daga @Enwagboso
Asali: Twitter

Wasu 'yan Najeriya sun nuna damuwarsu a kan wannan bidiyon mai tsawon dakika 27, hakan yasa ake ta bukatar Ikepazu ya ladabtar da Agbazuere.

Jama'a da dama sun koka da yadda ake watsa kudin tamkar takardu tare da take dokokin babban bankin Najeriya wanda ya hana watsawa tare da take kudi.

KU KARANTA: Kaothar Ajani: Marainiya mai shekaru 16 da ke tukin Napep don ciyar da kanninta

A wani labari na daban, Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, ya ce ya yi wuri shugabannin APC su fara magana a kan zaben shugaban kasa na 2023.

Ya fadi hakan ne a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba yayin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC.

Kashim ya bayyana hakan, inda yace ana karkatar da hankulan shugabanni a kan abubuwan da ke faruwa a kasa a halin yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: