Matashin likita tare da abokinsa sun kone kurmus a hatsarin mota a Katsina
- A ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, wasu abokai 2 suka tafka hatsari a hanyar Katsina zuwa Dutsin-ma
- Cikinsu, har da wani Likita mai suna Dr Sadiq Yahaya Zakka, tare da Abokinsa Auwal Shehu
- Kamar yadda rahotonni suka bayyana, motarsu ta kama da wuta sai da tayi kurmus da samarin
Wani mummunan lamari ya faru a titin Katsina zuwa Dutsinma a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba. Wasu abokai 2 suka mutu bayan motarsu ta kama da wuta, inda suka kone kurmus.
Al'amarin ya faru ne da misalin karfe 3pm lokacin da motarsu, kirar Toyota Camry ta kama da wuta.
Dr Sadiq Yahaya Zakka bai dade da gama karatunsa ba a wata jami'ar China, kuma yana ta shirye-shiryen zuwa bautar kasa, amma sai mutuwa ta dauke shi tare da abokinsa Auwal Shehu Danfaranshi.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 2, sun cafke 'yan fashi a Sokoto
Daya daga cikin wadanda suka yi hatsarin akwai wani matashi mai suna Fahad. Amma bai mutu ba don yanzu haka yana asibiti ana kulawa da lafiyarsa.
An birne Danfaranshi a ranar Lahadi da safe, 6 ga watan Disamba, kamar yadda musulunci ya tanadar.
KU KARANTA: Bidiyon COS na gwamna yana watsa wa fasto kudi a ofishinsa ya janyo cece-kuce
A wani labari na daban, jam'iyyar APC ta kara samun tabbacin cewa har yanzu 'yan Najeriya ita suke yayi, bayan ganin dumbin nasarorin da ta samu a zaben maye gurbi da aka yi, kamar yadda fadar shugaban kasa tace.
Malam Garba Shehu, babban hadimin shugaba Muhammadu Buhari a kan harkar yada labarai ya sanar da hakan.
A wata takarda da ya saki a Abuja ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, kakakin shugaban kasa yace hakika Shugaba Muhammadu Buhari ya yi matukar farinciki da jin nasarorin da APC ta samu a zaben maye gurbin da aka yi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng