Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa

Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa

- Alkalin kotun da Maryam sanda ta daukaka kara ya tsaya a kan tsohon hukuncin da aka yanke wa Maryam

- Ya tsaya a kan hukuncin da aka yanke mata ne bisa wasu kebabbun dalilai gamsassu guda uku

- Alkalin ya ce ya gamsu ita tayi kisan, sannan babu wani dalili da zai sa ta watsar da tsohon hukuncin

Daukaka karar da Maryam Sanda tayi na babbar kotu, a kan kisan mijinta da ake zargin ta yi a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba, shi ya fara janyo cece-kuce a Najeriya.

Kwamitin bincike na mutum 3, wanda Alkali Stephen Ada ya jagoranta, ta kori daukaka karar Sanda a ranar Juma'a.

Idan ba a manta ba, ana zargin Sanda da kashe mijinta, Bilyaminu Bello, wanda da ne ga dan uwan tsohon shugaban jam'iyyar PDP.

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu, bayan 'yan sanda sun kama ta dumu-dumu da laifin kisa a watan Nuwamban 2017.

KU KARANTA: 'Yan daba dauke da makamai sun tare Sanatan APC, sun bukaci N2m a take

Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa
Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa. Hoto daga ChannaleTv.com
Asali: UGC

Alkali Yusuf Halilu ya ce akwai duk wasu shaidu da ake nema, wadanda suka tabbatar da cewa Maryam Sanda ce ta kashe mijinta, garin dambensu ya fada kan tukunyar shisha ya mutu.

Bayan hukuncin ya janyo cece-kuce, Legit.ng ta bayyana dalilai 3 da suka sanya Alkali Halliru ya yanke mata hukuncin sakamakon yadda kwamitin binciken mutum 3 suka tabbatar da hakan.

1. Rashin iya maganar Sanda yayin daukaka karar, da kuma nuna lallai sai kotu ta jingine shari'ar da ta gabata, inda Sanda tace ba a yi mata adalci ba.

A cewarta, Alkalin ya nuna son kai, duk da duk wasu shaidu da ake nema duk an samu.

An yanke hukuncin ne bayan an samu shaidu kwarara, rashin magana mai dadi ga kotu, boye makamin da aka yi amfani dashi wurin kisan, sabawar maganganun shaidunta da kuma kin bayyana gaskiyar abinda ya janyo mutuwar mijinta.

2. Kamar yadda alkalin yace a ranar Jama'ar da ya yanke hukunci, babu dalilin da zai sa a share hukuncin da waccan kotun tayi, a yi wani daban.

Baya ga rashin nagartar Sanda, duk wasu shaidu da ake nema sun bayyana karara, wadanda suke nuna cewa ita ce take da laifi. Don haka dole ne kotu tayi adalci, babu wani rangwame.

3. Sanda ta kasa tabbatar wa da kotu cewa fasassar tukunyar shisha ce tayi ajalin mijinta. Duk da ta tsaya tsayin-daka a kan cewa abinda yayi ajalin mijin nata kenan, kwamitin binciken mutum-3 tace maganar kanzon kurege ce.

Alkalin ya ce hujjar Sanda ta yi kadan da ta gamsar da kotu cewa ba da gangan aka yi kisan ba.

KU KARANTA: Hotunan ranar daurin auren jarumi Nuhu Abdullahi da zukekiyar amaryarsa

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana yadda shugabannin tsaro suka dade a kan kujerunsu, inda yace ya kamata su tafi gida su huta, Daily Trust ta wallafa.

Kiraye-kiraye don cire shugabannin tsaro ya fara yawa ne tun bayan ganin yadda harkokin tsaro suka tabarbare.

Sanatan ya roki fadar shugaban kasa, inda ya bukaci a sauya su da wasu, bayan kashe-kashen manoman shinkafa na Zabarmari a jihar Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel