Zabarmari: A kan idona su ka yanka 'ya'yana guda biyu; mahaifin biyu daga cikin manoman da aka kashe
- Har yanzu ana cigaba da samun karin bayanai dangane da kisan kare dangi da aka yi wa dumbin manoma a jihar Borno
- A ranar Asabar ne mugayen 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram suka shiga gonakin kauyen Zabarmari tare da tafka muguwar barna
- Ba tare da girmama rai ko rayuwar dan adam ba, mayakan Boko Haram sun daure manoman, sun yankasu, sannan sun kone gonakinsu
Malam Abubakar Yunusa, ɗaya ne daga cikin waɗanda harin Zabarmari ya shafa, Uba ne da ya rasa ƴaƴansa biyu a mummunan harin da aka kai a garin Zabarmari, jihar Borno, kamar yadda The Nation ta wallafa.
Ya ce an kama shi da ƴa'ƴansa biyu sannan aka yi musu yankan rago akan idonsa.
"Mutane suna cikin aiki a gonakinsu, gaba ɗaya abin ya fara ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe, sai mayaƙan Boko Haram cikin kayan sojoji ɗauke da manyan bindigu suka yi mana ƙawanya suka zagaye mu."
KARANTA: Wata Jami'ar kasar Amurka ta dauki Ganduje aikin lakcarin a matakin Farfesa
"Sun yiwa ƴaƴana biyu yankan rago a gabana har ɗayansu ya tambayeni meye alaƙata da su?
"Sai na mayar masa da amsar cewa ƴaƴana ne, nine mahaifinsu. Har yanzu ina cikin alhini ta yadda mutane zasu zama marasa imani haka," a cewarsa.
Ya kara da cewa; "Sun hallaka mana makomar mu. Waɗanda aka kashe sune makomar rayuwarmu; Matasa ne ƙarfafa kuma a daidai lokacin cin moriyarsu".
"Ba zamu taɓa farfaɗowa daga wannan ɓarnar da aka yi mana ba, sun ƙarar da gabaɗaya matasan mu."
"Sun bar mu tsofaffi da alhini da wahalar marayun ƴaƴansu da matayensu" a cewarsa.
KARANTA: An kama Mohammed Usman, kasurgumin dan ta'addan da ya kashe shugaban APC na jihar Nasarawa
Acewar jaridar Daily Trust, manoman da suka haɗa da yara ƙanana da mata suna cikin girbar shinkafa a gonakinsu kusa da Zabarmari.
Zabarmari dai gari ne mai tazarar kilomita 25 zuwa babban birnin jihar Borno, Maiduguri aka far musu tsakani 9 na safe zuwa tsakar ranar Asabar.
An samu ƙarin bayanai ranar Lahadi game da yadda aka kashe mutanen.
Rahotanni sun yi nuni da yadda aka tasa ƙeyar mutanen daga gonakinsu da ƙarfin bakin bindiga, sannan aka kaisu can wani daban, aka yi tayi musu yankan rago ɗaya bayan ɗaya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta kalato bayanan.
Adadin bai ƙunshi mutane da dama da suka kashe a wurare daban daban ba da makusantan ƙauyukan.
Ba za'a iya shiga wuraren da suka yi ta'addanci ba sakamakon cinnawa gonakin wuta da suka yi, majiya mai ƙarfi, ciki har da shugabannin ƙauyuka da ƴan sintiri ne suka bayyana hakan.
A ranar Talata ne, Legit.ng Hausa ta rawaito cewar kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kisan dukkan manoman.
Kungiyar ta sanar da hakan ne a cikin sabon faifan bidiyo da ta fitar a ranar Talata, 01 ga watan Disamba.
A cikin faifan bidiyon, kungiyar ta sanar da cewa ta hallaka manoman ne saboda sun hada kai da jami'an tsaron gwamnati.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng