Gwamnoni suna so a san matsaya game da yankin da za a ba tikitin PDP a 2023

Gwamnoni suna so a san matsaya game da yankin da za a ba tikitin PDP a 2023

- Maganar yankin da za a kai takarar shugaban kasa a PDP ya kuma kara dawo wa

- Gwamnonin jam’iyyar suna so a tsaida magana ne domin hana wasu canza-sheka

- A dalilin haka gwamnoni suka shirya zama da masu harin takarar kujerar a 2023

Wasu gwamnonin jam’iyyar PDP sun fara kirkirar zama na musamman da manyan jam’iyya daga ciki har da tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.

Jaridar The Nation tace wadannan gwamnoni za su yi zama da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, domin a fara tsarin zabe mai zuwa a 2023.

Majiyar jaridar ta bayyana cewa makasudin wannan zama shi ne a fitar da yankin da za a kai takarar shugabancin kasa a jam’iyyar adawar a zaben 2023.

Hakan na zuwa ne bayan wasu daga cikin manyan ‘ya ‘yan PDP daga yankin kudu sun fara nuna damu wa game da makomar bangarensu a siyasar Najeriya.

KU KARANTA: 'Yan takarar PDP da APC da su ka shiga zaben cika gurabe

A dalilin wannan har PDP ta fara rasa wasu kusoshinta a yankin kudancin Kasar. The Nation ta ce hakan yasa gwamnonin jam’iyyar ke neman mafita tun wuri.

Ana zargin shugabannin PDP a karkashin Uche Secondus da yin sake da lamarin yankin da za a ba takara a zabe na gaba, wannan yasa gwamnoni suka tashi-tsaye.

“An kira taron kwatsam ne kawai bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya bar jam’iyya ya koma APC.” Wata majiya daga PDP ta zayyana wa manema labarai

Gwamnonin suna tsoron wasu takwarorinsu su bi Umahi zuwa APC tun da jam’iyyar hamayyar ta gaza tsaida magana, amma kusoshin Arewa suna ganin ana garaje.

KU KARANTA: Tinubu ya sasanta Aregbesola da ba a ga maciji da Gwamna Oyetola

Gwamnoni suna so a san matsaya game da yankin da za a ba tikitin PDP a 2023
Goodluck Jonathan da Atiku Abubakar Hoto: jonathangoodluck da Atiku.org
Asali: Facebook

Wata majiyar tace gwamnonin zasu gana da irinsu Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar da gwamnoni Aminu Tambuwal da Nyesom Wike sai Rabiu Kwakwanso.

Shugaban ‘yan Majalisar PDP, Kingsley Chinda ya huro wuta, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci a tunbuke shi daga mulki saboda halin rashin tsaro.

Kingsley Chinda a madadin ‘yan Majalisar PDP yana kiran a tsige shugaban kasa saboda a cewarsa, matsalar rashin tsaro ya addabi jama'a, gwamnati ta gaza komai.

Bayan kalaman Hon. Kingsley Chinda, APC tayi masa raddi, ta ce ba ta wannan ake yi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel