Gazawar shugaban kasa wurin bada tsaro abu ne da zai sa tsigesa, Osinbajo a 2015
- Sakamakon kashe-kashen da 'yan Boko Haram suke yi a Najeriya, mutane sun yi wani waiwaye adon tafi
- 'Yan Najeriya sun tunatar da mataimakin shugaban kasa, Osinbajo wata wallafa da yayi a Twitter a 2015 lokacin yana kamfen
- A ranar 8 ga watan Fabrairun 2015 ne Osinbajo yace in dai Jonathan bai iya kare rayukan al'umma ba, ya cancanci a tsige shi
Sakamakon kashe-kashen da 'yan Boko Haram suke tayi a Najeriya, 'yan Najeriya sun tunatar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a kan wata wallafarsa da yayi a 2015 a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.
Lokacin da Osinbajo yake kamfen a 2015, ya wallafa; "Idan shugaban kasa yace ba zai iya kulawa da rayuka da kuma dukiyoyin al'umma ba, tabbas laifi ne da yayi wanda ya cancanci a tsigeshi."
Ya yi wannan wallafar ne a ranar 8 ga watan Fabrairun 2015, wanda mutane suka yi ta tsokaci suna yabonsa.
A ranar Asabar, mayakan Boko Haram sun kashe fiye da mutane 43 a wata gonar shinkafa da ke kusa da Maiduguri jihar Borno, Vanguard ta wallafa.
KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta shirya taron NEC na gaggawa, ta bayyana rana
Kamar yadda AFP ta ruwaito, Boko Haram da ISWAP sun fara kai wa manoma, makiyaya da masunta hari, inda suke zarginsu da leken asiri da sanar da labaransu ga sojojin Najeriya, shiyasa sojojin suke kai musu farmaki.
A watan da ya gabata, AFP ta ruwaito yadda 'yan Boko Haram suka yi wa wasu manoma 22 yankan rago suna tsaka da noman rani a kusa da Maiduguri a hare-hare 2 daban-daban.
Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammad, ya ce yanzu haka Najeriya tana hannun 'yan ta'adda suna yadda suka ga dama saboda an hana Najeriya makamai don yakar 'yan ta'adda.
KU KARANTA: Abinda yasa rikicin APC na cikin gida yake ci gaba da kamari, DG na PGF
A wani labari na daban, Ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, a ranar Litinin yace a yanzu haka an bar Najeriya da 'yan ta'adda saboda an hana ta makaman yakar 'yan ta'adda duk da kokarin da takeyi wurin yakarsu.
Ministan ya nuna alhininsa a kan kisan manoma 43 na Zabarmari, karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, inda yace gwamnatin tarayya ba za ta zauna ba har sai ta kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng