Osinbajo: Burina in yi wa Najeriya aiki yanzu ba neman takarar Shugaban kasa ba

Osinbajo: Burina in yi wa Najeriya aiki yanzu ba neman takarar Shugaban kasa ba

- Yemi Osinbajo ya yi watsi da jita-jitar cewa ya na harin mulki a zaben 2023

- Mataimakin Shugaban kasar ya ce yanzu ba ya kawo takarar kasa a gabansa

- Farfesa Osinbajo ya ke cewa abinda ya sa gaba shi ne shawo kan matsalolin kasa

Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi fatali da rade-radin da wasu su ke yi na cewa ya na hangen mulki a zaben 2023.

Yemi Osinbajo ya fito ya yi magana game da wannan jita-jita da ya zagaye ko ina, ya ce a halin yanzu abin da ya ke kansa shi ne kokarin gyara Najeriya.

Da ya ke amsa tambayoyi a wajen taron kungiyar Lauyoyi na kasa watau NBA a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, 2020, ya ce babu tunanin 2023 a ransa.

“Ina mai matukar godiya ga damar da aka ba ni na yi wa Najeriya hidima, sannan yanzu abin da kurum ke gabana shi ne wannan aiki.” Inji mai girma Osinbajo.

KU KARANTA: Kalaman Bola Tinubu a 1997 za su kawo masa cikas a 2023

Osinbajo: Burina in yi wa Najeriya aiki yanzu ba neman takarar Shugaban kasa ba
Mataimakin Shugaban kasa Hoto: Twitter/ProfOsinbajo
Asali: Facebook

Farfesan ya ce akwai manyan ayyukan da ke gabansa da su ka sa ba ya waiwayen siyasar 2023. Na biyu a kasar ya ce tunaninsa kawai shi ne sauke nauyin da ya dauka.

A lokacin da ake tunanin Osinbajo zai gaji mai gidansa a 2023, sai ya ce, “Akwai abubuwan da ake bukatar a shawo kansu, kuma su ne na kawai a cikin lissafina yanzu.”

Mai girma Osinbajo ya yi wannan jawabi ne a matsayin martanin tambayar da ‘yanuwansa Lauyoyi su ka samu damar yi masa a kan abin da aka dade ana magana a kai.

Mataimakin shugaban kasar bai bayyana irin ayyukan da ya sa gaba ba, sai dai a matsayinsa, ya na cikin kusoshin tafiyar gwamnatin Buhari wanda za ta bar mulki a 2023.

A daidai wannan lokaci kuma mun ji cewa Yemi Osinbajo ya gana da malamai wadanda su ka kawo masa kuka game da dokar CAMA, ya ba su shawara abin da za su yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel