Najeriya ta mallaki dukkan abubuwan da za su iya kawo mata daukaka, Osinbajo

Najeriya ta mallaki dukkan abubuwan da za su iya kawo mata daukaka, Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriya tana da arziki

- Ya ce kasar nan ta tara duk wani abu da kowacce kasa take nema don ta daukaka

- Ya fadi hakan a ranar Talata a wani taro na NASIDRC da aka yi a Lafia, jihar Nasarawa

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriya tanada duk wasu abubuwan da ya kamata ta samu don ta daukaka.

Ya fadi hakan a ranar Talata, lokacin da ya je wata kaddamarwa ta NASIDRC a Lafia, jihar Nasarawa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Inda yace Najeriya tana da duk wani abu da kasa take bukata, tana da masu fasaha, maza da mata, masu tunani da ma'adanai iri-iri wadanda ake nema don kasa ta daukaka.

Najeriya ta mallaki dukkan abubuwan da za su iya kawo mata daukaka, Osinbajo
Najeriya ta mallaki dukkan abubuwan da za su iya kawo mata daukaka, Osinbajo. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matashin da ke samun 20,000 a wata ya siya wa budurwarsa abincin 4,500

"Gwamna Abdullahi Sule ya nuna halayen shugabanci nagari saboda cigaba da ayyukan da gwamnatin da ta gabacesa ta fara, Gwamna Umaru Tanko Al-Makura, na asibitin kwararru na Dalhatu Araf (DASH), Lafia.

"Jihar Nasarawa ba ta fi kowacce jiha arziki ba a Najeriya. Kuma idan aka dubi kudaden da Nasarawa take samu, da kuma wadanda ake bata, bata daya cikin jihohi 3 na sama," yace.

A wani labari na daban, mata masu gudun hijira daga kauyakun jihar Zamfara sun ce yunwa da sanyi zai iya ajalin su da yaransu, bayan 'yan bindiga sun kone musu gidajensu.

BBC Hausa ta ruwaito yadda fiye da mutane 500 daga kauyukun karamar hukumar Maru suke ta gararamba a tituna da sansanin gudun hijira na garin Mai Rairai, da ke jihar Kebbi.

Matan da suke sansanin 'yan gudun hijira tare da yaransu, sun ce ba su da abinci kuma 'yan bindiga sun kone musu gonakinsu, Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng