Fitaccen dan kasuwa, hamshakin mai kudi kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ya rasu

Fitaccen dan kasuwa, hamshakin mai kudi kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ya rasu

- Sanannen dan kasuwa Chief Harry Akande ya rasu a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba

- Ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya kamar yadda dan shi ya sanar a wata takarda

- Fitaccen mai arzikin ya kasance mai fatan tabbatar da zama Najeriya kasa ta gari da adalci

Fitaccen dan kasuwa kuma tsohon dan takarar kujerar shugabancin kasa, Harry Akande ya rasu. Dan kasuwan ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.

A wata takarda da dan sa mai suna Olumide Akande ya fitar a madadin iyalan, ya ce ya rasu a sa'o'in farko na ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya.

"Chief Harry Akande dan kasuwa ne sananne ba a gida Najeriya kadai ba har da kasashen ketare, yana da rinjaye a nahiyoyin duniya," takardar tace.

Fitaccen dan kasuwa, hamshakin mai kudi kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ya rasu
Fitaccen dan kasuwa, hamshakin mai kudi kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ya rasu. Hoto daga @Thisdaylive
Source: Twitter

KU KARANTA: Babban laifi ne cigaba da ajiye hafsoshin tsaro, Shekarau ya kalubalanci Buhari

Takardar ta kara da cewa, "abinda ya fi so a rayuwarsa shine ganin Najeriya ta zama kasa ta gari sannan adalci ya tabbata. Yana saka wa a ransa cewa hakan za ta faru babu dadewa."

An haifa marigayin a ranar 3 ga watan Maris 1943. ya halarci makarantar Olive Heights a Ibadan inda ya samu ilimin sakandare kafin ya tafi Amurka domin didigirinsa na farko da na biyu.

Ya dawo Najeriya a shekarun 1970 inda ya fara aiki. Ya kafa kamfaninsa mai suna Akande International Corporation a 1971, jaridar Thisday ta wallafa.

KU KARANTA: Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi

A fannin siyasa, yana daga cikin jiga-jigan da suka kafa jam'iyyar All Peoples Party (APP) wacce ta zamo jam'iyya ta biyu mafi rinjaye a Najeriya.

Akande ya nemi kujerar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar ANPP daga bisani.

A wani labari na daban, Ishaku Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa ya tsallake rijiya da baya.

Kamar yadda Legit.ng ta ga wata takarda wacce tazo daga ofishin yada labaran sanatan, wani mutum mai dauke da bindigar toka ya lallabo ya tare shi, inda yayi barazanar harbinsa matsawar bai bashi miliyan 2 ba.

Takardar, wacce hadimin sanatan a kan harkokin yada labarai, Michael Volgent ya saka hannu, ya ce al'amarin ya faru ne da misalin 2pm, inda matasa da yawa suka tare hanyar, yana hanyarsa ta zuwa bikin dan uwansa da ke Mubi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel