Rundunar sojin Najeriya ta matukar girgiza da kalubalen tsaro, Gwamnoni

Rundunar sojin Najeriya ta matukar girgiza da kalubalen tsaro, Gwamnoni

- NGF ta ce rundunar sojin Najeriya ta kidime a kan ta'addancin da ke addabar kasar nan

- Kuma bai kamata a sakar wa rundunar ragamar kawo karshen ta'addanci ba

- Ba za a iya dawo da wadanda suka mutu ba, amma idan ba a dakatar ba, asarar za ta nunku

NGF ta ce hankulan rundunar sojin Najeriya ya yi matukar tashi sakamakon tabarbarewar harkar tsaro a Najeriya, jaridar Vanguard ta wallafa.

A ranar Talata, hankalin NGF ya tashi kwarai a kan rashin tsaron da ke addabar kasar nan. Gwamnonin sun bayyana irin tashin hankali da kidimewar da suka shiga a kan yadda 'yan Boko Haram suka kashe manoma 43 a jihar Borno.

Wannan batun na NGF ya taso ne bayan JNI, karkashin mulkin sarkin musulmi na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya yi wani jan kunne jiya. Inda yace matsawar ba a kwace makamai kanana da manya ba da suke ta yawo a hannun 'yan ta'adda, kasar nan za ta cigaba da fuskantar barazana a harkar tsaro.

Rundunar sojin Najeriya ta matukar girgiza da kalubalen tsaro, Gwamnoni
Rundunar sojin Najeriya ta matukar girgiza da kalubalen tsaro, Gwamnoni. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Okorocha ga Buhari: Ka fatattaki dukkan masu mukami da hadimanka, sun gaza

Sannan babban malamin addinin kirista, Pope Francis, ya nuna alhininsa a kan kashe-kashen manoman Borno, kuma ya roki Ubangiji ya kawo karshen rashin tsaron da Najeriya take fuskanta.

A dayan bangaren,matasan Najeriya karkashin YPA ta yankin arewa, sun caccaki kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu jiya, bisa maganar da yayi a kan kisan manoman jihar Borno, wanda yace manoman basu samu amincewar rundunar soji ba kafin su je gonakinsu.

Yayin da shugaban NPF kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, yake jawabi a kan kisan manoman Borno, yace rundunar soji ta kidime a kan yadda za ta bullo wa matsalar rashin tsaro a Najeriya.

KU KARANTA: Basarake a Afrika ya zama mutum na 9 a duniya da yafi kowa yawan filaye

Fayemi ya kwatanta kisan da 'yan Boko Haram suka yi wa manoman Zabarmari ya zarce misali.

Ya ce matsalar rashin tsaron Najeriya ta wuce a sakar wa sojoji ragamar gabadaya.

NGF ta ce ba za su iya dawo da wadanda suka mutu ba, amma idan ba a kawo karshen wannan ta'addancin ba, da sannu zai zagaye kaf kasar kuma ya kashe nunkin wadanda suka mutu.

A wani labari na daban, TCN ta ce an gyara tashar rarrabe wutar lantarkin da ta samu matsala 'yan kwanakin da suka gabata, jaridar The Punch ta wallafa.

Mukaddashin darekta janar na TCN, Sule Abdulaziz ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba a Abuja.

Abdulaziz ya ce tun bayan aukuwar lamarin ranar Laraba, mintuna 40 kacal suka dauka kafin su kammala gyaran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel