Allah ba zai bar ka ba idan ka siya wa matarka mota, ka bar mahaifiyarka tana yawo a kasa, Mawaki
- Wani mawaki, dan Najeriya mai suna Duncan Mighty, ya bayyana ra'ayinsa a kan kyauta da kyautatawa ga iyaye
- A cewar Mighty, duk mutumin da ya siya wa budurwarsa mota, amma mahaifiyarsa tana tafe a kasa, zai sha azabar Ubangiji
- Haka kuma, duk masu tura wa 'yan matansu kudi da katin waya, yayin da iyayensu suke fama, kwarankwatsa sai ta ci su
Wani mawaki, dan Najeriya, mai suna Duncan Mighty, ya bayyana ra'ayinsa a kan kyautatawa a soyayya.
Mawakin ya ce duk mutumin da ya siya wa matarsa ko budurwarsa mota, amma ya bar mahaifiyarsa tana takawa da kafarta, zai fuskanci azabar Ubangiji.
Yace wannan azabar ba masu siyan mota kadai za ta shafa ba, har da masu tura wa 'yan mata da matansu kudi, amma kuma iyayensu suna rokonsu ko da kudin katin waya ne, amma suka hana su.
KU KARANTA: Dalilin da yasa na yi wa Shugaba Buhari takwara da tagwayen da na haifa, Gwamna Sule
Kamar yadda Duncan Mighty ya wallafa;
"Idan ka siya wa matarka mota, mahaifiyarka kuma tana tafiya a kasa, za ka fuskanci azabar Ubangiji.
"Idan kuma kana tura wa budurwarka katin waya da kuma kudi, amma mahaifiyarka tana fama da rashin kati a wayarta, kwarankwatsa ta fada maka. Duk inda kake, ka tsugunna ka sharara wa kanka mari."
KU KARANTA: Rayuwar Mahdi Shehu tana cikin garari, Iyalan babban dan kasuwa sun koka
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa a kan rashin damar bayar da umarni ga 'yan sanda a kan kashe-kashe da tabarbarewar tsaro a Najeriya.
A wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels suka yi da gwamnan a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, El-Rufai ya bayyana damuwar da shi da takwarorinsa na sauran jihohi suka shiga a kan harkokin tsaron kasar nan.
Gwamnan ya ce ana kiran gwamnoni da shugabannin jami'an tsaro ne a baki kawai, amma a zahiri, basu da damar tankwara 'yan sanda.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng