Hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Kano

Hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Kano

- Har ila yau, ana asaran rayuka a titunan Najeriya sakamakon hadarin mota

- Rashin kyawun hanya, karancin ma'aikata da kayan aiki babban tsaiko ne ga jami'an hukumar FRSC

- Direbobi na da nasu laifin na kure gudu a manyan hanyoyi

Mummunan hadarin motan da ya faru a Kwanar Garko dake karamar hukumar Garko ta jihar Kano, ya yi sanadiyar halakar akalla mutane 11, Daily Trust ta ruwaito.

Hadarin wanda ya faru daidai kauyen Dakare a hanyar Garko misalin karfe 10 na safiyar Alhamis tsakanin motoci biyu kirar Toyota Hiace da Volkswagen Sharon

Mutane takwas sun mutu nan take yayinda wasu uku suka cika a asibiti bayan an kaisu jinya.

An tattaro cewa yawancin matafiyan yan kasuwa ne da suke hanyar zuwa kasuwar Darki dake karamar hukumar Wudil.

Tabbatar da labarin, kakakin hukumar kiyaye hanyoyi da hadura FRSC na jihar, Kabiru Daura, ya ce mutane 20 hadarin ya shafa kuma 6 na kwance yanzu a asibiti.

KU KARANTA: Kar ka saki jiki, har yanzu akwai Korona, ko jiya Alhamis mutane 343 suka kamu

Hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Kano
Hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Kano
Source: Twitter

KU DUBA: An gurfanar da Maina a kotu, an mayar da shi gidan yari

A bangare guda, wani tsagin jam'iyyar APC a jihar Kano, a karkashin jagorancin Hussaini Isa Mairiga, ya sanar da sauke shugabannin tsagin jam'iyyar a karkashin jagorancin Abdullahi Abbas, kamar yadda Thecable ta rawaito.

An sake zaben shugabannin tsagin jam'iyyar APC da ke karkashin jagorancin Abbas a shekarar 2018 saboda rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar a shekarar 2017.

Tsagin da Abbas ya ke jagoranta shine mai daurin gindin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar ganduje.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel