Kar ku saki jiki, har yanzu akwai Korona, ko jiya Alhamis mutane 343 suka kamu
- Da alamun mutane sun fara sakin jiki kan lamarin annobar Korona duk da cewa daruruwan yan Najeriya na sake kamuwa da cutar kulli yaumin
- Gwamnatin tarayya ta shawarci masu shirye-shiryen bikin Kirismeti su bi hankali
- Hukumar NCDC ta bayyana adadin wadanda suka kamu da cutar ranar Alhamis a fadin tarayya
Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 343 ranar Alhamis a cewar alkaluman hukumar kiwon lafiya, NCDC.
Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 68,303 a Najeriya.
Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Alhamis , 4 ga watan Disamba, 2020.
Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.
Daga cikin mutane sama da 68,000 da suka kamu, an sallami 64,291 yayinda 1179 suka rigamu gidan gaskiya.
Ga jerin adadin wadanda suka kamu a jihohin Najeriya:
FCT-123
Lagos-106
Kaduna-72
Nasarawa-14
Rivers-5
Bauchi-4
Imo-4
Ogun-4
Ekiti-3
Edo-2
Oyo-2
Plateau-2
Akwa Ibom-1
Kano-1
KU KARANTA: Gwamnatin Borno ta biya N600,000 ga kowanne cikin iyalan manoma 48 da aka kashe
Ga jerin jiha-jiha:
KU DUBA: Majalisa: Watakila mu ga zuwan Shugaban kasa a ranar 10 ko 15 ga watan nan
A wani labarin daban, Iyalan kowanne cikin manoma 48 da aka kashe a gonan shinkafa a jihar Borno ya samu kudi N600,000 daga hannun gwamnatin jihar Borno.
Hakazalika sun samu buhuhunan kayan abinci daga kwamitin da gwamna Babagana Umara Zulum ya nada domin raba kayan tallafin.
Kudin ya samu ne daga hannun Kungiyar gwamnonin Arewa, da suka bada gudunmuwan N20m, yayinda hukumar cigaban Arewa maso gabas NEDC ta bada N5m, rahoton Thisday.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng