Yanzu-yanzu: An gurfanar da Maina a kotu, an mayar da shi gidan yari

Yanzu-yanzu: An gurfanar da Maina a kotu, an mayar da shi gidan yari

- An koma gidan jiya, kotu ta garkame AbdulRashid Maina a gidan yari

- An gurfanar da shi a kotu ne bayan taso keyarsa daga kasar Nijar ranar Alhamis

- Ana zarginsa da almundahanan kudin yan fansho sama da naira bilyan biyu

Bayan watanni uku da bashi beli, an mayar da AbdulRashid Maina kotu da safiyar Juma'a, 4 ga watan Disamba, 2020.

An gurfanar da shi gaban Alkali Okong Abang.

Alkalin ya bada umurnin garkameshi a gidan yari har sai an kammala shari'arsa.

Hakan ya biyo bayan bukatar da lauyan hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Mohammed Abubakar, ya gabatar.

Mun kawo muku rahoton cewa hukumar yan sandan Najeriya ta dawo da AbdulRashid Maina, gida bayan guduwar da yayi zuwa kasar Nijar.

Hukumar ta bayyana hakan ne da ranar nan a shafinta na Tuwita.

Tace: "Hukumar yan sanda ta dawo da AbdulRashid Abdullahi Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran aikin fansho, yau, 3 ga Disamba, 2020 daga Niamey, jamhurriyar Nijar."

"An shigo da tsohon shugaban fanshon Najeriya cikin jirgin yan sanda mai lamba 5N-HAR kuma ya sauka daidai karfe 14:17 na ranar."

KU KARANTA: EndSARS: Gwamnan Legas ya baiwa kowanne cikin iyalan yan sandan da aka kashe N10m

A ranar 18 ga Nuwamba, 2020, Alkali Abang ya janye belin da ya baiwa Maina kuma ya bada umurnin daureshi.

Bayan an nemi Maina an rasa, Alkali ya ce a garkame Ndume a kurkuku maimakonsa ko ya biya kudi N500m.

Bayan kwana hudu da tsare Ndume, Alkali Abang ya bada belin Sanatan.

Alkali Okon Abang a hukuncin da ya yanke ranar Juma'a ya ce ya baiwa Sanata Ndume beli ne saboda tarihinsa na halayya mai kyau, amma ba dan uzurorin da ya gabatar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel